Kakakin kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO Mista Keith Rockwell, ya yabawa sabon tsarin bude kofa da Sin za ta dauka, wanda shugaban kasar Xi Jinping ya gabatar cikin jawabinsa a wajen dandalin shekara-shekara na Asiya na Boao.
Da yake zantawa da manema labarai, Keith Rockwell ya yabawa jawabin shugaba Xi mai taken "Bude kofa ga kasashen waje don samun ci gaba tare, sa kaimi ga aikin kirkire-kirkire don samun makoma mai haske". A ganinsa, tsarin bude kofa ga kasashen waje da Sin take dauka zai kyautata halin da duniya ke ciki, da daidaita sabanin ra'ayin da ake samu tsakanin al'ummun duniya.
An gudanar da dandalin Asiya na Boao na shekara-shekara na bana daga ranar 8 zuwa 11 ga wannan watan, inda dandalin na wannan karo mai taken "Asiya mai bude kofa da kirkire-kirkire da duniya mai wadata da bunkasuwa" ya samu halartar wakiali 2000 daga kasashe ko yankuna 63. (Amina Xu)