Kakakin hukumar Mista Huang Songping ya ce, tattalin arzikin Sin ya samu bunkasuwa yadda ya kamata a cikin watanni Jarairu, Fabrairu da Maris, lamarin da ya habaka bukatun shigowa da kayayyaki, saboda haka yawan danyen mai, da gas, da tagulla da dai sauran kayayyakin yau da kullum da Sin ke shigowa da su ya karu.
A cikin wadannan watanni, yawan kayayyakin da Sin ta shigo da su ya karu da kashi 4.3 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, kana rarar kudin cinikayya ta ragu da kashi 21.8 bisa dari, wanda dai ya nuna cewa cinikayyar shige da fice na kasar Sin na samun daidaito. (Amina Xu)