in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta inganta amfani da na'ura mai kwaikwayon tunanin dan Adam a Jami'o'i
2018-04-13 10:07:34 cri
Kasar Sin za ta matse kaimi wajen inganta amfani da na'ura mai kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI a jami'o'i.

Ma'aikatar ilimi ta kasar da ta bayyana haka, ta fitar da wani jadawali dake cewa, Jami'o'in kasar Sin za su inganta amfani da tsarukan da za su dace da kirkire-kirkiren kimiyya musammam samar da na'ura mai kwaikoyon tunanin dan Adam na zamani ya zuwa shekarar 2020. Sannan ya zuwa 2030 kuma, za su zama jigo cikin cibiyoyin samar da na'urar a fadin duniya, wadanda za su iya samarwa kasar Sin fasahohi da kwararru.

Jadawalin na neman hada na'urar da darussan da suka shafi kimiyyar kumfyuta da lissafi da physics da nazarin halayya da zamantakewar dan Adam. Haka zalika, ya na bukatar kara inganta bincike da kafa karin cibiyoyin samar da na'urar masu karfi, tare da samun hadin kan kasashen duniya.

A cewar jaridar Science and Technology Daily ta kasar Sin, jami'o'i 19 ne suka kara darussan nazarin halayyar dan Adama da sarrafa bayanai.

Har ila yau, wani shiri da hukumomi ciki har da ma'aikatar ta ilimi suka shirya da za a fara a wannan watan na Afrilu, na da burin bada horo kan na'urar AI, inda zai taimaka wajen horar da malaman jami'o'i 500 da dalibai 5,000 cikin shekaru sama da 5. (Fa'iza Msuatpha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China