in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar kolin Rwanda ta bi sahun Kenya na amincewa da yarjejeniyar ciniki ta CFTA
2018-04-13 09:03:13 cri
Majalisar zartaswar kasar Rwanda ta amince da yarjejeniyar dokar kafa tsarin ciniki maras shinge na kasashen Afrika wato (CFTA), inda matakin ya baiwa majalisar dokokin kasar damar amincewa da yarjejeniyar.

Cikin batutuwan da aka tattauna a lokacin taron majalisar kolin kasar a ranar Laraba, majalisar ta kuma amince da kafa wasu ka'idoji da suka shafi cinikin kayayyaki, da ka'idojin da suka shafi ayyukan hidima, da kuma dokoki da ka'idojin da suka shafi warware takaddamar ciniki wadanda aka rattaba hannu kansu a Kigali, babban birnin Rwanda, a watan Maris na shekarar 2018.

Yarjejeniyar ciniki maras shinge ta Afrika zata kara bunkasa sha'anin cinikayya a tsakanin kasashen nahiyar.

Sama da kasashe 44 ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a Kigali a lokacin taron kolin shugabannin kasashe mambobin kungiyar AU karo na 10.

Za'a aiwatar da yarjejeniyar ta CFTA bayan an samu kasashe akalla 22 da suka amince da ita.

Ana sa ran yarjejeniyar ciniki ta CFTA zata baiwa mutane sama da biliyan 1.2 damar cin gajiyar harkokin cinikayyar.

Masana harkokin tattalin arziki suna hasashen yarjejeniyar zata kara habaka hada hadar ciniki, da masana'antu, da gina kayayyakin more rayuwa, da kuma fadada hanyoyin tattalin arzikin kasashen.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China