Mr. Tuju wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayin zantawar sa da kamfanin dallancin labarai na Xinhua, ya ce nahiyar Afirka na fuskantar dumbin matsaloli, amma duk da haka, nasarorin da Sin ta cimma sun zamo darasi ga nahiyar, game da aiwatar da dabarun samun bunkasa.
Ya ce aiwatar da gyare gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, cikin shekaru 40 da kasar Sin ta sashe tana yi, su ne suka ba ta damar zamowa kasa ta 2 mafi karfin tattalin arziki a duniya, kuma ta daya a jerin kasashe dake tallafawa ci gaban tattalin arzikin duniyar baki daya.
A daidai wannan lokaci da kasar ke cika shekaru 40 da fara aiwatar da gyare gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, Sin za ta ci gaba da fadada kasuwannin ta, za ta kuma kara samar da damammaki na zuba jari, da karfafa kiyaye ikon mallakar fasaha, tare kuma da bullo da dabarun fadada shigo da kayayyaki.
Jami'in ya kara da cewa, abu ne mai matukar muhimmanci Sin ta kara fadada bude kofofin ta na kasuwanci. Wadannan matakai za su tabbatar da wanzuwar hada hadar cinikayya tsakanin ta da sauran kasashen dake nahiyar Afirka bisa salo na cudanya tsakanin sassan biyu. (Saminu)