Ana fatan wannan banki zai sa kaimi ga raya hadin gwiwar hada-hadar kudi a tsakanin Sin da Afirka.
Shugaban kasar Congo Brazzaville Denis Sassou-Nguesso ya halarci bikin. Kaza lika kuma mataimakiyar shugaban bankin aikin gona na Sin da Congo Brazzaville madam Guo Ningning ta bayyana cewa, an kafa bankin Afirka na Sin da Congo Brazzaville a kasar Congo Brazzaville ne, domin gudanar da aiki a yankin tsakiyar nahiyar Afirka, da samar da gudummawa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Congo Brazzaville, da raya hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasar Congo Brazzaville. (Zainab)