Kungiyar kananan hukumomi ta nahiyar Afrika ta bukaci kasashen nahiyar su daukaka tsarin sakarwa matakan gwamnati mara don ba nahiyar damar cimma muradun ci gaba masu dorewa.
Sakatare janar na hadaddiyar kungiyar birane da kananan hukumomi ta Afrika Jean Pierre Elon Mbassi, ya bayyana wa Xinhua cewa, sakarwa matakan gwamnati mara zai taimaka wajen kai muhimman ayyuka kamar na kiwon lafiya da ilimi kusa da al'umma.
Sakatare janar din ya bayyana haka ne yayin taron kungiyar na yankin gabashin Afrika, inda ya ce, ya kamata ba matakan gwamnati iko ya zama abun da gwamnatocin Afrika suka sanya gaba, domin zai taimaka wa nahiyar cimma akasarin muradun ci gaba masu dorewa da take burin samun.
Taron na yini biyu ya mai da hankali ne kan nazarin nasarorin da aka samu game da ba matakan gwamnati iko a Afrika. (Fa'iza Mustapha)