Game da hakan, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, matakan da kasar ta dauka, sun taimaka matuka ga habakar cinikayya, gami da ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.
Muhimman matakan da shugaba Xi ya sanar, sun nuna cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu ya zama babban zarafi ga duk duniya, abun da kowace kasa za ta iya cin alfanunsa.(Murtala Zhang)