Shugaba Xi Jinping ya bayyana hakan ne a yau Talata, yayin zantawar sa da firaministan kasar Holland Mark Rutte, yayin taron shekara na Boao na kasashen Asia.
Xi Jinping ya ce ya kamata kasar sa da Holland su ci gaba da yunkurin su, na bunkasa tattalin arzikin duniya da ke bude kofa ga juna, kana su kare salon cinikayya da sauran kasashen duniya yadda ya kamata. A hannu guda kuma su goyi baya, tare da yayata tsarin gudanar da cinikayya da zuba jari maras shinge.