in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi: Sin za ta kara fadada damar shiga kasuwanninta
2018-04-10 13:54:49 cri

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya fada a yau Talata cewa, kasar za ta kaddamar da wasu matakan sauye sauye a cikin wannan shekara, wadanda za su kara fadada damammakin shiga kasuwannin kasar, kasar Sin za ta inganta yanayin zuba jari ga masu sha'awar zuba jari daga kasashen waje a kasarta, kasar Sin za ta karfafa dokokin dake ba da kariya ga ikon mallakar fasaha, kasar Sin za ta aiwatar da wasu tsare tsare da nufin fadada hanyoyin da take shigo da kayayyaki daga kasashen waje.

Xi, ya yi wannnan tsokaci ne a lokacin gabatar da jawabin bude taron dandalin Boao na Asiya na wannan shekara.

Kasar Sin ta fara aiwatar da manufofinta na yin gyare gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje ne tun a shekarar 1978, kuma al'ummar Sinawa sun tsaya tsayin daka wajen sadaukar da kai domin gina ci gaban kasa a cikin shekaru 40 da suka gabata, in ji shugaba Xi Jinping.

"A yau, al'ummar Sinawa suna iya yin alfahari ga manufofin kasar Sin na yin gyare gyaye a cikin gida da bude kofa ga waje, sauye sauyen da kasar Sin ta samu ba wai sun samar da bunkasuwa ga kasar kadai ba ne, har ma sun amfanawa duniya baki daya."(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China