in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanin tattalin arziki: Asiya za ta ci gaba da zama yanki mafi saurin bunkasuwar tattalin arzki a duniya
2018-04-10 13:22:30 cri

Ana gudanar da taron shekara shekara na dandalin Boao na shekarar 2018 a lardin Hainan na kasar Sin. Masana tattalin arzikin Sin da waje sun bayyana jiya Litinin 9 ga wata cewa, a cikin shekaru 20 masu zuwa har zuwa tsakiyar wannan karni, ko shakka babu Asiya za ta zama yanki mafi saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya. Kuma Sin za ta sanar da sabbin matakan da za ta dauka ta fuskar bude kofa ga kasashen waje a yayin dandalin, lamarin da ya fi jawo hankalin bangarorin daban-daban.

A gun karamin dandali mai jigon "Yin hasashe kan tattalin arzikin Asiya" da aka yi a ranar 9 ga wata, tsohon shugaban babban bankin kasar Sin Mista Dai Xianglong ya nuna cewa, a cikin shekaru 20 masu zuwa har zuwa tsakiyar wannan karni, ko shakka babu Asiya za ta ci gaba da zama yanki mafi saurin bunkasuwar tattalin arziki a duniya. Ya ce:

"A cikin shekaru 20 da suka gabata, matsaikacin saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasashen Asiya ya kai kashi 6.8 cikin dari a kowace shekara, saurin zai ci gaba a cikin shekaru 20 masu zuwa. Babban dalili shi ne, ingancin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, saurin bunkasuwar Indiya, da kuma kyakkyawan hadin kai tsakanin Sin, Japan da Korea ta kudu. Ban da wannan kuma, shawarar 'ziri daya da hanya daya' za ta samar da sabon zarafi ga bunkasuwar tattalin arzikin Asiya."

Yayin da yake tabo maganar makomar tattalin arzikin kasar Sin, Mista Dai ya ce, saurin bunkasuwar tattalin arzikin Sin ya sami dan raguwa a shekarun baya-bayan nan, wannan bai haifar da koma baya ba, ya kasance tsarin da Sin take dauka da kanta don kyautata ka'idar bunkasuwa. A ganinsa, Sin za ta mai da hankali kan ingancin bunkasuwar tattalin arzikinta a nan gaba. Ya ce:

"Da farko dai, Sin tana yin kwaskwarima kan tsarin samar da kayayyaki da daina samar da kayayyaki maras inganci. Ban da wannan kuma, za ta sa kaimi ga bunkasa fasahar zamani a wannan fanni. Na biyu, za ta kyautata tsarin samar da kudade, da tsarin samar da gidaje, ta yadda za a kawar da kalubale a wannan fanni."

A ganinsa, ta wadannan hanyoyi, tattalin arzikin Sin zai samu bunkasuwa mai dorewa.

A gun wannan dandali, sabbin matakan bude kofa ga kasashen waje da Sin za ta sanar sun fi jawo hankalin al'ummun kasashen duniya. Babban sakantaren kungiyar masana'antu da kasuwanci ta kasar Indiya Mista Sanjaya Baru ya ce:

"Saboda karuwar yawan kudin shiga da kudin da aka kashe wajen sayen abubuwa, Sin na da karfi sosai wajen habaka bukatunta na shigo da kayayyaki daga sauran kasashe, ciki har da kasashe masu tasowa. Idan Sin ta kara shigo da kayayyaki daga kasashen waje da kara zuba jari ga kasashen waje, hakan zai kawo amfani matuka ga bunkasuwar tattalin arzikinta, har ga sauran kasashe masu tasowa."

Ban da wannan kuma, masana mahalarta taron sun bayyana cewa, bunkasuwar tattalin arzikin Asiya na fuskantar kalubaloli da dama, ciki har da takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka. Shugaban cibiyar nazarin tattalin arzikin kasar Sin Mista Fan Gang ya ce:

"Kayayyakin da Sin take fitarwa zuwa Amurka, na kunshe da kayayyakin da Sin take shigowa da su daga sauran kasashen Asiya, alal misali, wasu kayayyakin latironi daga Korea ta kudu, wasu sassan injuna daga Japan da Malaysia, wasu daga kasashen kudu maso gabashin Asiya. An sake hada wadannan kayayyaki a Sin, daga baya Sin ta fitar da su zuwa Amurka. Takaddamar cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka a wannan karo zai kawo illar ga sauran kasashe." (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China