in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da Kenya sun sha alwashin kyautata mu'amalar ciniki da tattalin arziki a tsakaninsu
2018-04-10 09:39:56 cri
Kasashen Sudan da Kenya sun bayyana aniyarsu na kyautata mu'amala a tsakaninsu, musamman ta fuskar dangantakar tattalin arziki.

An bayyana sanarwar ne bayan wata tattaunawar da aka gudanar tsakanin mataimakin shugaban kasar Sudan Bakri Hassan Saleh, da mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto, wanda ke ziyarar aiki a Khartoum.

A cikin jawabin da ya gabatar a yayin tattaunawar tasu, Bakri Hassan Saleh ya ce, a shirye suke su yi aiki tare da juna wajen inganta dangantakar tattalin arziki da ciniki a tsakaninsu, kana da samar da sabbin hanyoyin ci gaba domin amfanin kasashen biyu, musamman ma tun bayan dage takunkumin tattalin arzikin da aka kakabawa kasar ta Sudan.

Ya kuma bayyana damuwar kasar ta Sudan sakamakon yawaitar tashe tashen hankula dake ci gaban da wanzuwa a makwabciyarta Sudan ta kudu, inda ya bukaci kasashen Afrika da su hada gwiwa wajen kawo karshen halin matsin rayuwa da al'ummar Sudan ta kudun ke fama da shi.

A nasa bangaren, William Ruto, ya nanata aniyar kasar Kenya wajen cimma nasarar wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta gabashin Afrika.

Da yake jawabi a yayin tattaunawar Ruto ya ce, kasar Kenya ta shirya tsab domin bada gudunmowarta karkashin shirin nan na samar da zaman lafiya a kasashen Somaliya, Kongo da Sudan ta kudu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China