in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta ce tana iya maido da samar da sinadarin Uranium cikin sauri
2018-04-09 13:08:14 cri

Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliyar kasar Iran (AEOI), Ali Akbar Salehi, ya sanar a jiya Lahadi cewa, idan kasashen yamma suka yi watsi da yarjejeniyar makaman nukilyar kasar Iran, kasar za ta maido da samar da nukiliya mai inganci cikin kwanaki hudu.

Ya ce, wannan sako ne ga kasar Amurka, sai dai bai yi wani karin haske ba.

Kasar Iran dai ta jima da yanke kudurin yiwuwar sauya matsayinta kan yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma tsakaninta da Amurka a shekarar 2015, ya kara da cewa, "Muna fatan Amurkar ba za ta yi watsi da yarjejeniyar ba tun da ta kasance babban kalubale a gare su ta fuskar kimiyya."

Salehi ya bayyana shugaban Amurka Donald Trump a matsayin dan kasuwa wanda yake kokarin daga matsayin ajandarsa ta kasa da kasa ta hanyar yanke wasu kudurori marasa alkibla.

Trump ya sha nanata cewa, zai dage wasu daga cikin takunkuman da Amurkar ta azawa Iran game da yarjejeniyar nukiliyar, da tsaurara dokokin bincike, da takaita shirin Iran na kera makamai masu linzami.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China