Da yake zantawa da manema labarai bayan ya ziyarci sansanin 'yan gudun hijira ta Gihembe dake lardin Gicumba dake arewacin Rwanda, Flippo Grandi ya ce za su gwada sabbin dabaru, inda za su tuntubi shirin samar da abinci na duniya game da neman taimako.
Ya ce akwai bukatar a kara karfafawa kokarin gwamnatin Rwanda na taiamkawa 'yan gudun hijira, yana mai cewa akwai bukatar ba 'yan gudun hijirar damar yin aiki da sauran hidimomi.
A cewar hukumar tunkarar annoba da kula da harkokin 'yan gudun hijira ta Rwanda, sansanin Gihembe na bada mafaka ga 'yan gudun hijirar kasar Congo kimanin 12,000.
Minista mai kula da hukumar Jeanne d'Arc de Bonheur, ya ce samun dawwaumammiyar mafita ya dogara ne ga karfafawa 'yan gudun hijirar ta yadda za su iya kula da kansu, ta hanyar horar da su fasahohi don kirkiro ayyukan yi, zuwa lokacin da za a samu zaman lafiya a kasarsu ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. (Fa'iza Mustapha)