in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Rwanda: shawarar "ziri daya da hanya daya" zai karfafa gwiwar nahiyar Afirka
2018-04-09 10:27:31 cri

Charles Kayonga, Jakadan Rwanda da ke nan kasar Sin, ya bayyana cewa, aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" ya dasa harsashi mai inganci wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama, kana zai karfafa gwiwar nahiyar Afirka wajen hada kan kasashenta da kuma raya su tare.

Yayin da yake zantawa da manema labaru a ranar 7 ga wata a nan Beijing, jakadan ya yi nuni da cewa, kasarsa ta Rwanda tana cibiyar nahiyar Afirka, kuma tana da dimbin damarmaki da ba a amfana da su a harkokin sufuri, inda ya ce kasar ta kasance tamkar mahada ta dinke nahiyar Afirka baki daya. A matsayinta na abokiya mafi girma a harkokin ciniki, kuma wadda ta fi zuba jari a Afirka, har kullum kasar Sin na kokari tare da kasashen Afirka wajen habaka hadin gwiwarsu a fannonin ciniki da zuba jari, musamman ma raya tsarin hanyoyin dogo a gabashin Afirka karkashin shawarar "ziri daya da hanya daya", da kuma gaggauta aikin hadewar kasashen Afirka gaba daya, sun samar wa kasashen na Afirka sabon zarafi wajen samun moriyar juna da ci gaba tare, lamarin da zai taimaka musu samun kyakkyawar makoma.

Har ila yau, jakadan ya kara da cewa, kasashe 44 na Afirka sun daddale yarjejeniyar kafa yankin ciniki cikin 'yanci a Afirka a birnin Kigali na kasar Rwanda a ranar 21 ga watan Maris na bana, lamarin da zai kara azamar yin ciniki tsakanin kasashen Afirka, haka kuma zai kara inganta mu'amala a tsakanin kasashen Afirka da kuma abokansu ta fuskar ciniki a kasar Sin da sauran kasashe. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China