Kamfanin ya tabbatarwa kafafen yada labarai na kasar cewa, al'amarin ya auku ne bayan ramin ya rufta a wani wurin da kamfanin ke aikin hakar ma'adinai a yankin Ahafo, dake da nisan kilomita 307 daga arewa masu yammacin birnin Accra.
Wata sanarwar da Newmont, kamfanin mafi girma na biyu wajen hakar zinare a duniya ya fitar, ta ce Mutane 8 ne ke aiki cikin ramin a lokacin da ya rufta
Wadanda suka mutun ma'aikata ne na kamfanin Consar da aka ba kwangilar gina saman ramin hakar zinare din da ya rufta.
An kwashe sauran ma'aikatan da suke wurin, tare da dakatar da aikin har zuwa lokacin da Newmont ya gamsu cewa za a iya fara aiki ba tare da wata matsala ba.
Tuni hukumomi suka fara bincike kan lamarin. (Fa'iza Mustapha)