in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin muhimmin ginshiki ne a tsarin shugabancin duniya
2018-04-08 13:28:35 cri
Kafin ya tashi zuwa kasar Sin don yin ziyara gami da halartar taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na kasashen Asiya na Bo'ao, babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya zanta da manema labarai, inda ya ce, dimbin nasarorin da kasar Sin ta samu a cikin shekaru arba'in da suka gabata bayan da ta fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje, sun sa kasar ta kara taka muhimmiyar rawa kan tsarin shugabanci na duniya, kana, ta zama babbar ginshiki a tsarin tafiyar da harkokin duniya.

Guterres ya ce, babban taken taron na bana na dandalin tattaunawa na Bo'ao shi ne, tsarin bude kofa da ci gaban fasahohi na nahiyar Asiya, da bunkasuwar duniya baki daya. Wannan ya shaida cewa, dandalin tattaunawa na bana, ba ma kawai zai maida hankali kan ci gaban nahiyar Asiya ba ne, har ma zai maida hankali kan ci gaban duka duniya baki daya.

Guterres ya kara da cewa, kasar Sin tana taka rawar a-zo-a-gani a fannonin inganta hadin-gwiwa tsakanin kasashen dake tasowa, da kuma cimma muradan samar da dawwamammen cigaba na MDD nan da shekarar 2030. Haka kuma, shawarar 'ziri daya da hanya daya' da gwamnatin kasar Sin ta gabatar, ba ma kawai na da babbar ma'ana ga kasashen dake tasowa ba ne, har ma tana da ma'ana sosai ga habaka gami da hadin-gwiwar tattalin arzikin duk duniya baki daya.

A waje guda kuma, Antonio Guterres ya ce, ra'ayin bada kariya ba hanya madaidaiciya ba ce da za'a iya bi wajen warware matsalar tattalin arzikin duniya. Ya ce, yana goyon-bayan dunkulewar duk duniya baki daya da kuma tsarin gamayyar cinikayya na kasashen duniya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China