in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hanyar daidaita takaddamar cinikayya mafi dacewa ita ce maida martani
2018-04-08 11:37:23 criJiya Asabar 7 ga wata, wasu masanan tattalin arzikin kasar Sin sun bayyana a nan birnin Beijing cewa, dalilin da yasa kasashen Sin da Amurka suke fuskantar takaddamar cinikayyar dake tsakaninsu yanzu shine domin Amurka ta dauki matakai da basu dace ba, a don haka hanyar daidaita takadama mafi dacewa itace kasar Sin ta mai da nata martanin.

Kwanan baya, ofishin wakilan cinikayyar Amurka ya sanar da aniyar kasar ta kara kudaden haraji a kan jerin kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasar Amurkar, wanda adadin kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 50 wato kwatankwacin karin harajin na kashi 25 bisa 100 ke nan, daga baya gwamnatin kasar Sin ta dauki wasu matakai domin maida martani, ban da haka, a ranar 5 ga wata, gwamnatin Amurka ta sake sanar da cewa, zata ci gaba da kara kudaden haraji ga kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasar, wanda adadin kudinsu zai kai dalar Amurka biliyan 100, cikin sauri ne gwamnatin kasar Sin ta bayyana cewa, ita ma zata kara daukan wasu sabbin matakai domin mai da martani.

Masanin harkar kudin kasar Sin Guo Kai yana mai cewa, Amurka ce ta tayar da takaddamar cinikayya bisa binciken data gudanar kan babi na 301 na dokar cinikayyar kasar Amurka ta shekarar 1974, hakan bai dace ba, dole ne a daidaita takaddamar, kuma hanya mafi dacewa ita ce kasar Sin ta maida nata martani, a cewarsa, "Dalilin da yasa kasashen biyu wato Sin da Amurka suke fuskantar takadamar cinikayya shine domin Amurka ta gudanar da bincike bisa babi na 301 na dokar cinikayyar data tsara a shekarar 1974, idan ka duba rahoton da aka fitar bayan binciken, abu ne mai sauki ka iya lura cewa, sakamakon da aka samu bashi da tushe, makasudin fitar da rahoton shine domin kara kudaden haraji kawai, bisa labaran da wasu kafofin watsa labarai na kasar Amurka suka watsa, an ce, shugaba Trump ya taba bayyana cewa, 'ban kula da ikon mallakar fasaha ba, abun da nafi mai da hankali shine kara kudaden haraji', a don haka a bayyane ne an gano cewa, Amurka ta tada takadamar, a karkashin irin wannan yanayi, hanya mafi dacewa itace kasar Sin ta maida nata martanin. Ina ganin cewa, sau tarin yawa ne gwamnatin kasar Sin ta taba nuna matsayinta na yin shawarwari, amma Amurka bata yarda ba, kawo yanzu maida martanin itace hanya daya tilo dake gabanmu."

Kafin wannan, kasar Sin ita ma ta yi gargadi cewa, babu wanda zai samu moriya daga takadamar cinikayya. Hakika tun bayan shekarar 1975 har zuwa yanzu, Amurka tana fama da gibin kudi yayin da take gudanar da cinikayyar waje, masanin harkar kudin kasar Sin Ha Jiming ya bayyana cewa, "Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyaran fuska kan tattalin arzikinta da bude kofa ga ketare, musamman ma tun bayan data shiga kungiyar ciniki ta duniya, 'yan kasuwan kasashen ketare da dama sun kafa kamfanoni a kasar Sin, hakan yasa kasar Sin ta kasance kasar dake da manyan kamfanonin samar da kayayyaki na kasashen duniya, idan kasar Amurka ta kayyade fitar da wasu kayayyaki, musamman ma kayayyakin da ake samarwa ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani zuwa ga kasar Sin, ko shakka babu lamarin zai kawo illa ga moriyar kanta, idan Amurka ta kara fitar da irin wadannan kayayyaki, to gibin kudin dake tsakanin sassan biyu zai ragu a bayyane cikin sauri."

Ha Jiming ya kara da cewa, kara kudaden haraji ba zai taimakawa Amurka yayin da take kokarin daidaita matsalar gibin kudi ba, har zai lahanta moriyar kanta.

Masanin harkar kudin kasar Sin Guan Tao ya jaddada cewa, kasar Sin tana da kasuwa mai girma, wadda ke taka muhimmiyar rawa kan ci gaban tsarin cinikayya dake tsakanin sassa da dama a fadin duniya, a cewarsa, "Ina ganin cewa, kasar Sin bata son ganin irin wannan yanayin da ake ciki, Amurka ce ta tada takaddamar, hakika kasar Sin tana fatan bayar da gudumowarta ga cigaban tattalin arzikin duniya ta hanyar bude kasuwarta, hakan shi zai taimakawa cigaban tsarin cinikayya tsakanin sassan da dama a fadin duniya."

Duk da cewa, Amurka tana kalubanlatar kasar Sin ta hanyoyi daban daban, kana tana daukan matakan kara kudaden haraji ga kayayyakin kasar, amma kasar Sin ba ta jin tsoro ko kadan, tabbas ne za ta dauki sabbin matakai domin mai da nata martanin, tare kuma da kare moriyar kasar da moriyar jama'ar kasar, a sa'i daya kuma, zata ci gaba da gudanar da gyaran fuska kan tattalin arziki da bude kofa ga kasashen ketare, ta yadda zata kara taka rawa wajen ci gaban tattalin arzikin duniya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China