in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kusan dakaru 1,900 ne za su halarci atisayen soji da Amurka ke daukar nauyi a Afrika
2018-04-07 11:58:05 cri
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce kusan dakaru 1,900 ne daga kasashe 20 na Afrika da na yammacin duniya, za su shiga cikin rawar dajin soji da ake yi kowacce shekara a nahiyar Afrika.

Rawar dajin da aka yi wa lakabi da "Flintlock" atisaye ne na soji da Amurka ta kirkiro a shekarar 2005, don sojoji horo kan dabarun tunkarar ta'addanci.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Amurkan ta fitar a jiya, ta ce za a gudanar da atisayen na bana ne a wurare daban-daban ciki har da Niger da Burkina Faso da Senegal daga ranar 9 zuwa 20 ga watan nan na Afrilu.

Sanarwar ta kara da cewa, Flintlock na daya daga cikin manyan atisaye na musammam na rundunar sojin Amurka dake aiki a nahiyar Afrika.

Dakarun da za su shiga cikin atisayen sun hada da na kasashen Burkina Faso da Kamaru da Chadi da Mali da Mauritania da Niger da Nijeriya da Senegal da kuma wasu kasashe 12 na yammacin duniya. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China