in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FM: Idan bangaren Amurka ya fitar da kayayyaki kirar kasar Sin da zai karbi karin harajin kwastam a kan su, nan da nan bangaren Sin zai mayar da martani mai matukar karfi
2018-04-06 22:03:24 cri
A yau da dare a nan Beijing, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayar da amsa ga wasu tambayoyin da aka yi masa, dangane da kalaman Shugaba Donald Trump na Amurka, na duba yiwuwar kara harajin da yawansa ya kai dala biliyan 100, kan karin wasu hajojin da Sin ke sayarwa Amurka.

An tambaye shi cewa, a ran 5 ga wata bisa agogon gabashin kasar Amurka, shugaban kasar Amurka ya fitar da wata sanarwa, wadda ke kunshe da muradin sa na dudduba yiyuwar kara harajin da yawansa zai kai dalar Amurka biliyan 100 kan karin wasu hajojin da Sin ke samarwa Amurka, shin ko me bangaren Sin ke gani kan kalaman na sa?

Mr. Lu Kang ya ce, a gani na bangaren Amurka ya yi kuskure wajen nazarin halin da ake ciki yanzu, har ma ya dauki mataki da sam bai dace. Daga karshe dai matakin da bangaren Amurka ya dauka zai lahanta moriyar kasar. Yanzu kuma bangaren Sin a shirye yake kamar yadda ya kamata, idan bangaren Amurka ya fitar da takardar sunayen kayayyakin da zai kara harajin da yawansa zai kai dalar Amurka biliyan 100, tabbas ne babu tantama ko kadan, bangaren Sin zai fitar da matakin mayar da martani nan da nan. Mun riga mun gaya wa bangaren Amurka cewa, kada ya bari naman jini wurin babe.

An kuma tambaye shi cewa, a ganinsa mene ne asalin wannan yakin cinikayya da ake yi tsakanin Sin da Amurka?

Mr. Lu Kang ya ce, a ganinmu wannan gwagwarmaya ce da ake yi tsakanin matakin kashin kai na Amurka, da tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori da dama, kuma gwagwarmaya ce da kasar Amurka take amfani da matakin kashin kai domin tunkarar ka'idodin yin cinikayya tsakanin kasa da kasa cikin 'yanci. Idan an bata ka'idodin yin hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama, da yin cinikayya cikin 'yanci, tabbas hakan zai lalata kokarin bunkasa tattalin arzikin duk duniya bai daya, ya kuma haifar da illa sosai ga kokarin farfadowar tattalin arzikin duk duniya. Ba ma kawai za a kawo illa ga moriyar kasar Sin ba, har ma za a kawo illa ga duk duniya gaba daya. A yayin wannan muhimmiyar matsala, dole ne mu yi gwagwarmaya.

Sannan akwai wani dan jarida da ya tambaye shi, idan bangaren Amurka ya kara daukar matakin tsananta halin da ake ciki, wane irin matakin mayar da martani kasar Sin za ta dauka?

Mr. Lu Kang ya bayyana cewa, ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta riga ta bayyana a fili cewa, a shirye muke wajen daukar matakan tinkarar tsananta halin da ake ciki na kasar Amurka, har ma mun riga mun tsara matakan mayar damartani filla filla. Mun riga mun ce, bangaren Sin ba zai tayar da hankali ba, amma ba zai yarda da wani ya tayar da hankali kamar yadda yake so ba. Tabbas ne za mu dauki matakin tinkarar shi. Mu Sinawa mu kan cika alkawarin da muka dauka. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China