in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manoman waken soya a Amurka sun bukaci Trump ya dauki matakan da suak dace dangane da batun haraji tsakaninsa da kasar Sin
2018-04-06 12:46:11 cri
Kungiyar manoman waken soya ta Amurka, ta bukaci shugaban kasar Donlad Trump, ya warware takaddamar cinikayya dake tsakaninsa da kasar Sin bisa hanyoyin masu ma'ana maimakon yin illa ga muradun manoman.

Da yake tsokaci game da sabbin matakan da kasar Sin ta sanar da dauka yayin da takaddamar cinikayya tsakaninta da Amurka ke kara kamari, wanda ya hada da karawa waken soyan Amurka haraji da kaso 25, shugaban kungiyar manoman ya ce har yanzu da sauran lokacin gyara matsalar, domin kasar Sin ta ce za ta fara amfani da harajin ne la'akari da lokacin da gwamnatin Trump ta fara amfani da matakanta.

Sanarwar da shugaban kungiyar kuma manomi a jihar Iowa John Heisdorffer ya fitar, ta ce suna kira ga shugaba Trump ya warware matsalarsa da kasar Sin bisa hanyoyin da suka dace da za su haifar da kyakkyawan sakamako ga manoman waken soya.

Ya kara da cewa, kamata ya yi gwamnatin Trump ta lalubo hanyoyin rage gibin da ke akwai ta hanyar kara takara, maimakon yin shinge ga kasuwannin kasashen waje. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China