in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi kira da a kara kare tsarin cinikayya a fadin duniya
2018-04-06 12:30:40 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce matakan cinikayya masu tsauri da Amurka ta dauka zai kawo nakasu ga cinikayya da tattalin arzikin duniya, kuma ya kamata kasashen duniya su hada hannu wajen kauracewa irin wadanan matakai, don raya ci gaban tattalin arzikin duniya.

Yayin wani taron manema labarai bayan ganawarsa da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a jiya, Wang Yi dake ziyara a Rasha, ya ce matakin baya-bayan nan da Amurka ta dauka ya sabawa dokokin kungiyar kula da cinikayya ta duniya WTO, kuma barazana ne ga tubalin tsarin cinikayya na duniya, wanda zai yi mummunan tasiri a kan ci gaban harkokin cinikayya da tattalin arzikin duniya.

A ranar Talata da ta gabata ne gwamnatin Amurka ta gabatar da jerin kayayyakin da karin haraji na kaso 25 cikin dari zai shafa, wadanada suka hada da kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa kasar da darajarsu ta kai dala biliyan 50. Inda a wani mataki na mayar da martani, ita ma kasar Sin a ranar Laraba, ta bayyana jerin kayayyakin Amurka da ke shigowa kasar da darajarsu ta kai dala biliyan 50, wadanda za ta karawa harajin kaso 25 cikin dari, ciki har da motoci da sinadarai da kuma waken soya.

A cewar Wang Yi, a masatyinta na kasa mai cikakken iko da halaltaccen 'yancin kare kanta, kuma mai goyon bayan tsarin cinikayyar duniya, an tilastawa kasar Sin daukar matakan kare kanta daga harajin da Amurka ta gabatar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China