in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Trump na Amurka ya yi barazanar kara harajin biliyan 100 kan hajojin kasar Sin
2018-04-06 12:05:30 cri
Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa ya nemi ofishin wakilin harkokin cinikayyar kasarsa, da ya duba yiwuwar kara harajin da yawansa ya kai dala biliyan 100, kan karin wasu hajojin da Sin ke shigarwa Amurka, a wani mataki da ka iya kara rura wutar takaddamar cinikayya dake wakana tsakanin kasashen biyu, tare da jefa ci gaban tattalin arziki cikin hali na rashin tabbas.

Wata sanarwa daga fadar White House, ta rawaito shugaban na Amurka na cewa "Duba da yadda Sin ta maida martani ga Amurka bisa rashin adalci, na baiwa ofishin walikin cinikayya umarnin duba yiwuwar sanya karin haraji da zai kai dala biliyan 100, karkashin tanajin sashe na 301, idan kuma hakan ta yiwu, a nazarci kayayyakin da harajin zai shafa," (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China