in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ba za ta mika wuya sakamakon matsin lamba da ake yi mata ba
2018-04-04 21:04:20 cri

Da safiyar yau Laraba ne ofishin wakilan cinikayyar Amurka, ya wallafa wani bayani a shafin sa na yanar gizo, inda ya sanar da aniyar Amurka game da kara kudaden haraji a kan jerin kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasar, wanda adadin kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 50, wato kwatankwacin karin harajin kashi 25 bisa 100 ke nan.

Bayan gwamnatin kasar Amurka ta gabatar da wannan mataki, gwamnatin kasar Sin ita ma ta yanke shawarar kara haraji da kaso 25 cikin dari kan nau'o'in kayayyaki 106, karkashin wasu rukunoni 14, wadanda suka hada da kayan amfanin gona, da motoci da jiragen sama, da dai sauransu.

Jami'an ma'aikatar harkokin kudi, da na ma'aikatar harkokin kasuwanci na kasar Sin sun bayyana a birnin Beijing cewa, tuni kasar Sin ta riga ta nuna hakurinta game da wannan yanayi, amma idan kasar Amurka ba za ta dakatar da wannan batu a kan lokaci ba, to Sin za ta dauki matakai daidai da na Amurka kamar yadda doka ta tanada, wadanda tabbas ne za su ba Amurka wahala.

A yayin taron manema labaran da aka kira a yau Laraba dangane da wannan harka, mataimakin ministan harkokin kasuwancin kasar Sin Wang Shouwen ya bayyana cewa: "Bisa dokar cinikin ketare ta kasa da kasa, kasar Sin za ta mai da martani kan dukkan takunkumin da sassa daban daban suka kakaba mata ta fuskar ciniki. Shi ya sa, kasar Sin ta gabatar da jerin karin haraji kan kayayyakin Amurka, wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 50. Amma, ana iya cewa, Sin ta riga ta nuna hakurinta kan wannan harka."

A wannan rana kuma, Zhu Guangyao, mataimakin ministan kudi na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta dau fansa ne sakamakon tilasta mata da aka yi. Ta girmama bukatar da manomanta suke da ita, za ta kara haraji kan waken soya da take shigowa da shi daga kasar Amurka. A ganinsa, kasashen 2 sun gabatar da bukatunsu a kan tebur ne kawai, yanzu lokaci ya yi da za a yi shawarwari tsakanin kasashen biyu."Ba tare da wata rufa-rufa ba, bisa kididdigar da aka samu, yawan waken soya da kasar Sin ta shigo da shi daga Amurka, ya kai kashi 62 cikin dari, bisa jimillar waken soyan da Amurka ke fitarwa. Sannan yawan waken soya da kasar Sin ta shigo daga kasar Amurka ya kai kashi 34.39 cikin dari, bisa jimillar waken soya da kasar Sin ta shigo da shi daga ketare a shekarar 2017. Amurka sayar wa kasar Sin waken soya mai tarin yawa. Sakamakon haka, manoman kasar Sin wadanda suke noman waken soya sun kai kara cewa, kudin alawus da gwamnatin kasar Amurka take biyan manomanta, ya haifar da illa ga moriyar manoman kasar Sin. Har yanzu matakin dau fansa da kasar Sin za ta dauka bai fara aiki ba. Bangarorin biyu sun gabatar da bukatunsu a kan tebur ne kawai, amma yanzu lokaci ne na shawarwari tsakanin kasashen biyu, bisa sharadi daya, wato dole ne su mutunta juna. Bai kamata ko wane bangare ya sanya wani sharadi na ba gaira ba dalili ba."

Dangane da damuwar da ofishin wakilin Amurka kan harkokin ciniki ya nuna cikin rahotonsa na bincike mai lamba 301 kan shirin kasar Sin "Kirar kasar Sin 2025", Wang Shouwen, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya ce, shirin kasar Sin ya dace da ka'dojin kungiyar ciniki ta duniya wato WTO. Kasar Sin ba ta boye komai ba, kuma tana bude kofarta ga kowa da kowa, ba ta nuna bambanci ba. Tana maraba da kamfanonin Sin da kasashen waje da su shiga wannan shiri.

Babu wanda zai ci nasara cikin matsalar ciniki. A matsayin mambar WTO da ke sauke nauyi bisa wuyanta, kasar Sin ba ta so samun matsalar ciniki a tsakaninta da sauran kasashe, amma ba ta ji tsoron daidaita matsalar. Zhu Guangyao ya ce,"Yanzu dukkan kasashen 2 sun gabatar da sharuddansu a fili. Muna fatan kasashen 2 za mu girmama juna da nuna wa juna sahihanci. Za mu iya yin tattaunawa tare bisa ka'idar hadin gwiwa domin samun nasara tare. Idan Amurka ta ci gaba da nuna taurin kai, to kuwa kasar Sin ba za ta ja da baya ba, duk da matsin lambar da kasashen waje suka rika yi mata tun bayan kafuwar sabuwar kasar Sin. Tarihin jamhuriyar jama'ar kasar Sin, tarihi ne na bunkasuwar kasar ta Sin, kuma tarihi ne dake kunshe da yadda jama'ar Sin suka yi gwagwarmaya. Kasar Sin ba za ta mika wuya sakamakon matsin lamba da kasashen waje suka yi mata ba."

Har ila yau, Zhu Guangyao ya ce, nan gaba kasar Sin za ta kara bude kofarta ga kasashen waje. (Maryam Yang &Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China