Da yammacin yau Laraba ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa a nan birnin Beijing.
Yayin zantawar tasu, Li Keqiang ya yi nuni da cewa, gwamnatin Sin na karfafa gwiwar kamfanoninta masu karfi, da su yi hadin gwiwar kasuwanci a Zimbabwe. Kaza lika gwamnatin Sin na fatan nuna goyon baya, da taimako ga Zimbabwe, wajen raya tattalin arziki da zaman al'ummar kasar, a kokarin samun moriyar juna da nasara tare. (Tasallah Yuan)