Yau Laraba ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron manema labaru a nan Beijing cewa, har kullum gwamnatin kasar Sin na bukatar kamfanonin kasar dake ketare, su rika bin dokokin kasashen da suke hada-hada, kuma rika sada mazauna wurin da alherai, a kokarin samun moriyar juna da nasara tare.
Mr. Geng ya ce kasar Sin na fatan yin kokari da kasar Mozambique, wajen ci gaba da raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 yadda ya kamata.
Kwanan baya, hukumar Amnesty International ta kaddamar da wani rahoto dake cewa, wani kamfanin kasar Sin da aiki a Mozambique, ya gaza wajen kare muhalli kamar yadda dokokin wurin suka bukata, wanda hakan ya haddasa gurbatar muhallin wurin, tare da haifar da illa ga zaman rayuwar mazauwn wurin. (Tasallah Yuan)