in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakin Trump na kara haraji zai lahanta moriyar Amurka
2018-04-04 16:10:13 cri

Da safiyar yau Laraba ne ofishin wakilan cinikayyar Amurka ya wallafa wani bayani a yanar gizonsa, inda ya sanar da aniyar kasar ta kara kudaden haraji a kan jerin kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasar, wanda adadin kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 50 wato kwatankwacin karin harajin na kashi 25 bisa 100 ke nan.

Bisa bayanin ofishin, an samu wannan jerin sunaye ne bayan kididdigar da aka yi ta kamputa, al'amarin da zai kara lahani ga 'yan kasuwar kasar Sin dake fitar da kaya zuwa ketare, kuma hakan zai kiyaye moriyar kamfanonin kasar Amurka. Amma, idan aka duba abubuwan dake cikin bayanin, za a gano cewa, Amurka ta dauki wannan mataki ne ba gaira-ba sabar, abun da zai yi illa ga kasashen biyu.

Kayayyakin dake cikin bayanin jerin sunayen ya kunshi wasu sinadarai masu guba, wadanda Sin ba za ta fitar zuwa Amurka ba. Saboda akwai yiwuwar wadannan sinadarai za su gurbata muhalli, hakan ya sa Sin ta kayyade fitar da irin wadannan abubuwa. Ban da wannan kuma, saboda bunkasuwar tattalin arziki, Sin za ta kara bukatar irin wadannan sinadarai, kayyade shigar da irin wadannan kayayyaki da Amurka ta yi ba zai kawo illa ga kasar Sin ba ko kadan.

Game da kayan karafa da na gorar ruwa, kasar Sin ba ta fitar da su da yawa zuwa Amurka. To, idan gwamnatin Trump tana son kare sana'arta ta mulmula kayan karafa, kara sanya haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasar, sam bai isa ba. Amma idan aka dubi halin da ake ciki yanzu, Trump na nan na kokarin cire takunkumin da gwamnatinsa ta sanyawa sauran wasu kasashe, kuma makasudinsa a bayyane yake, wato yana son kulla kawance da su don gudanar da yakin cinikayya da kasar Sin. Kasar Sin ta fahimci abun da Trump ya yi, kuma a ra'ayinta, abun da ya yi sam ba zai taka rawa ba wajen kare sana'ar Amurka ta fannin mulmula karafa.

Sa'an nan an sanya kayayyakin injuna da na lantarki cikin jerin kayayyakin da za a kara karbar harajin kwastam kansu, wadanda da yawa daga cikinsu suka kasance abubuwan da jama'ar kasar Amurka ke bukata a zaman rayuwarsu. Yanayin da kasar Amurka ke ciki a fannonin fadin kasa da yadda al'ummar kasar ke rabuwa a wurare daban daban, da al'adun gargajiyarsu, da yadda albashin ma'aikatan kasar ya yi yawa idan aka kwatanta da na sauran kasashe, duk wadannan bangarori a hade suke kuma sun tabbatar da cewa, jama'ar kasar suna da dimbin bukatu kan wasu kayayyakin da suka hada da karamin janaraito, da na'urorin lantarki, gami da wasu na'urorin gyaran tsarin abubuwa. Sai dai a cikin gidan Amurka ba a samun isashen kamfanoni masu samar da irin wadannan kayayyaki, kana kayayyakin da suke samarwa na da tsada sosai. Saboda haka za a iya hasashen yadda rikicin ciniki zai yi tasiri kan zaman rayuwar jama'ar Amurka, musamman ma ga wadanda ke da matsakaici da karamin karfi.

Idan Amurka ta maida batun shigar da injin da na'ura mai kwakwalwa ke sarrafawa, da mutum-mutumin inji na masana'antu, da batir irin na Lithium, da sassan inji na motoci masu amfani da karfin wutar lantarki na kasar Sin a cikin jerin sunayen kayayyakin da aka saka takunkumi don yin takara a dogon lokaci, abin mamaki shi ne, aikin zai daga kudin kera kayayyaki a cikin Amurka, domin kamfanonin kera kayayyaki na kasar suna amfani da wadannan kayayyaki da na'urorin da aka shigar da su daga kasar Sin. Idan aka gaza yin amfani da kayayyaki da na'urorin masu inganci da arha, za a rage karfin kayayyakin da kasar Amurka ke samarwa.

Gaskiya akwai riba mai tsoka ga dimbin kayayyaki masu dauke da sinadarai da aka kara sanya haraji a kai, kuma kamfanonin kasar Amurka za su amfana kwarai idan an ba su kariyar ciniki a wannan fanni. Sai dai ba kadai a Amurka kayan ke da kasuwa ba, domin suna da babbar kasuwa a sauran sassan duniya.

A game da matakan da Amurka ta dauka, tuni kasar Sin ta mai da nata martani, inda ta ce za ta dauki matakai daidai da na Amurka kamar yadda doka ta tanada. Ana ganin cewa, matakan da kasar Sin ta dauka ma ka iya ba Amurka wahala, wadanda har za su kara hura wutar matsalolin da ke addabar tattalin arzikinta, har ma za su iya kawo illa ga siyasar gwamnatin Trump.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China