in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Zimbabwe sun lashi takobin karfafa alakarsu
2018-04-04 12:16:35 cri

Jiya Talata, a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Zimbabwe, wanda a yanzu haka yake ziyara kasar, Emmerson Mnangagwa, inda suka kuduri aniyar kara daga matsayin dangantakar kasashen biyu, zuwa dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkanin fannoni.

Da maraicen jiya Talata, shugaba Xi Jinping ya shirya bikin maraba da zuwan Mnangagwa kasar Sin, wadda ta kasance ziyarar farko da Mnangagwa ya kai wata kasa da ba ta Afirka ba tun bayan da ya hau karagar mulkin Zimbabwe a watan Nuwambar bara. A yayin shawarwarinsu, Xi Jinping ya ce Mnangagwa tsohon amini ne na kasar Sin, inda ya ce:

"Tun a lokacin baya har zuwa yanzu, akwai alakar kut da kut tsakanin kasashen gami da jam'iyyun mulkin Sin da Zimbabwe. Kasashen biyu na girmama juna da kara samun fahimtar juna ta fannin siyasa, har ma hadin-gwiwarsu ta fannin tattalin arziki da cinikayya ta samu manyan nasarori. A sabon yanayin da ake ciki, ci gaban alakar kasashen biyu na fuskantar sabon zarafi. Ina fatan yin kokari tare da takwarana Mnangagwa don kafa alkibla ga hadin-gwiwar kasashenmu, don kara samar da alheri ga jama'armu."

Xi ya jaddada cewa, ya kamata Sin da Zimbabwe su ci gaba da nunawa juna goyon-baya da samun fahimtar juna a wasu muhimman batutuwa, da fadada hadin-gwiwa kan shawarar 'ziri daya da hanya daya', da sauran wasu bangarorin da suka jibanci ababen more rayuwar jama'a da ayyukan gona da harkokin kudi. Haka kuma, Xi ya yi kira ga kasashen yammacin duniya da su kyautata dangantakarsu da Zimbabwe tun da wuri, don tallafawa kasar wajen samun ci gaba.

Emmerson Mnangagwa, mai shekaru 75 a duniya, ya taba zuwa nan kasar Sin karatu a shekarun 1960, har ma ya taba kai ziyara kasar Sin a matsayin shugaban majalisar dokoki tare da mataimakin shugaban kasarsa. A watan Nuwambar bara, Mnangagwa ya zama shugaban kasar Zimbabwe, inda Xi Jinping ya tura wakilinsa don ziyartar kasar, duk abubuwan da suka burge shi matuka. A wajen shawarwarin, Mnangagwa ya ce:

"Gwamnatin Zimbabwe da jama'arta gami da ni kaina, muna godewa kasar Sin saboda goyon-bayan da ta ba mu bayan da aka mika ragamar mulkin kasarmu cikin lumana. Muna kuma yaba maka saboda hangen nesa da ka yi, da taya ka murnar bullo da tunaninka na tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin na sabon zamani. Bayan da Zimbabwe ta samu 'yancin kai, ta kulla dangantaka tare da kasar Sin, kuma Zimbabwe ta dukufa wajen raya wannan dangantaka mai dadadden tarihi. A waje daya kuma, jam'iyyar ZANU-PF mai mulki a Zimbabwe gami da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suna da kyakkyawar alaka tsakaninsu, muna godewa kasar Sin saboda dimbin goyon-baya da taimakon da ta ba mu."

Mnangagwa ya ce, kasarsa ta dade tana tsayawa haikan kan manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duk fadin duniya, kana, tana son kara kyautata dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkanin fannoni da kasar Sin, musamman a fannonin da suka shafi cinikayya, zuba jari, kimiyya da fasaha, fasahar sadarwa, ababen more rayuwar jama'a da kuma musanyar al'adu.

Har wa yau, Zimbabwe za ta yi kokarin kara dankon zumunci tsakanin kasar Sin da nahiyar Afirka, da jinjinawa gwamnatin kasar saboda muhimmiyar shawarar da ta fitar, wato 'ziri daya da hanya daya'. Zimbabwe na matukar goyon-bayan karfafa hadin-gwiwa a karkashin tutar tsarin FOCAC, wato dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka, da goyon-bayan kasashen Afirka su shiga cikin ayyukan da suka shafi shawarar 'ziri daya da hanya daya'.

Game da hadin-gwiwar Sin da kasashen Afirka, shugaba Xi Jinping ya ce, kasar Sin za ta himmatu tare da sauran kasashen duniya don raya sabuwar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da raya kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkan bil'adama, da kuma inganta hadin-gwiwa tare da kasashen dake tasowa, ciki har da kasashen nahiyar Afirka.

Shugaba Xi Jinping ya sake nanata cewa, ko ta yaya, kasar Sin za ta tsaya tare da kasashen Afirka, da zama babbar aminiyar arziki ta Afirka.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China