in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tarayyar Africa: Nahiyar Afrika na cikin jimamin mutuwar Winnie Mandela
2018-04-04 09:48:13 cri
Shugaban hukumar Tarayyar Afrika AU Moussa Faki Mahamat, ya ce nahiyar Afrika na cikin jimamin mutuwar Winnie Madikizela-Mandela.

Cikin wata sanarwar da ya fitar, Moussa Mahamat ya ce matsayin Winnie Mandela wadda ke alamta fafutukar kawo karshen wariyar launin fata a Afrika ta kudu abu ne da ba za a taba mantawa da shi, kasancewarta 'yar gwagwarmaya mara tsoro, wadda ta sadaukar da mafi yawan rayuwarta wajen samarwa Afrika ta Kudu 'yanci.

Shugaban na AU ya ce baki dayan tarayyar na taya al'ummar nahiyar jimamin mutuwar Winnie Madikazela-Mandela, wadda ta jajirce wajen kawo karshen wariya da rajin tabbatar da hakkoki da walwalar mata a kasarta.Ya kuma mika ta'aziyya ga Gwamnati da al'ummar kasar Afrika ta Kudu.

Winnie Mandela mai shekaru 81 da ta mutu a Johannesburg na Afrika ta kudu a ranar Litinin da ta gabata, ta taba auren tsohon shugaban kasar marigayi Nelson Mandela wanda ya yi fice wajen yaki da wariyar launin fata a kasar.(Fa'iza Musatpha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China