in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana da mabiya addinai kimanin miliyan 200
2018-04-03 16:07:37 cri

Wata takardar bayanai da majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar a yau Talata ta nuna cewa, akwai mabiya addinai da yawansu ya kai mutane miliyan 200 da kuma malaman addinai sama da 380,000 a kasar.

Addinai mafiya shahara a kasar Sin sun hada da na mabiya addinin Buddah, da Tao, da Musulunci, da darikar Catholica, da kuma na Protestan, kamar yadda takardar bayanan mai taken manufofin kasar Sin game da ba da kariya da 'yancin bin addinai ta tabbatar da hakan.

Takardar ta nuna cewa, mabiya addinin musulunci su ne kanana kabilu 10 a kasar wadanda ke da mabiya sama da miliyan 20, da kuma malaman addinin musulunci kimanin 57,000.

A halin da ake ciki a yanzu, akwai wuraren ibadu masu rajista kimanin 144,000 a fadin kasar Sin, daga cikinsu akwai na mabiya addinin Buddah 33,500, akwai masallatai 35,000, da cocin katolika 6,000 da cocin Protestant 60,000, in ji sanarwar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China