in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masanin tattalin arzikin Kenya: Manufar kariyar ciniki babu amfani, Afrika na son kara hadin gwiwa da kasar Sin
2018-04-03 13:50:06 cri

Kwanan baya, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da karawa kasar Sin harajin dala biliyan 60 da kuma takawa kamfanonin kasar Sin birki wajen zuba jari a Amurka, wanda ya jawo hankalin kasa da kasa. Shahararriyar masaniyar ilimin tattalin arzikin kasar Kenya Anzetse Were ta ce, manufar kariyar ciniki zai kawo illa ga bangarori masu ruwa da tsaki, kasashen Afrika ma suna son kara hadin gwiwa da kasar Sin.

Madam Anzetse Were ta fadawa manema labarai cewa, takadamar cinikayya da Amurka ta haddasa babu shakka ya kasance mataki maras Imani ga duk yanayin tattalin arzkin duniya. Har ma wannan mataki zai kawo babbar illa ga tattalin arzkinta. Ta ce:

"Wannan mataki zai kawo illa ga bangarorin daban-daban ba ma kawai ga kasar Sin ba. Sin ta kan fitar da wasu kayayyakin latironi zuwa Amurka, amma wasu matakan samar da wadannan kayayyaki an riga an raba su ga kasashen Asiya ko sauran yankuna har ma da Turai, hakan ya sa Amurka ta kara dorawa kasar Sin haraji zai kawo illa ga dukkan wadannan kasashe. Ban da wannan kuma, yawancin 'yan kasar Amurka suna sayen kayayyakin da aka shigo daga Sin, matakin zai haddasa hauhawar farashin wadannan kayayyaki a cikin gidan Amurka."

A ganin madam Anzetse Were, abin da ya haddasa takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka shi ne rashin daidaito tsakanin cinikayyar kasashen biyu, sa'an nan Amurka ta yi kuskure tana ganin cewa gibin ciniki da take da shi mai girma nada alaka da kasar Sin ne kawai. Amma a hakika dai tsarin ciniki da Amurka take gudanar da shi maras daidaito shi ya kasance muhimmin dalilin da ya haddasa matsalar. A cewar madam Anzetse Were:  

"Wasu kayayyakin Amurka ba su da karfin takara mai inganci idan aka kwantanta da na kasar Sin, shi ya sa Trump ya yanke wannan hukunci. Abin da ya sa gaban Amurka yanzu shi ne tsai da wani shirin da ya iya kara karfin takarar kayayyakin da Amurka za ta kera a nan gaba. Babu amfanin kara dorawa kayayyakin kasar Sin haraji."

Madam Anzetse Were ta kara da cewa, abin da manufar kariyar ciniki zata kawo shi ne rufe kofa kawai, shi ya sa samar da yanayi cikin 'yanci da adalci mataki ne mai kyau wajen kara bunkasa ciniki tsakanin kasashen biyu. Manufar bude kofa da mutunta kasashe daban-daban da Sin take dauka na samun karbuwa sosai a Afrika. Hadin gwiwa da Sin take yi da kasashen Afrika na samun ci gaba sosai a shekarun baya bayan nan . Ta ce:

"Afrika na fatan gudanar da ciniki tare da kasashen daban-daban cikin 'yanci. Shi ya sa kasashen Afrika na maraba da masu zuba jari daga kasar Sin, don taimaka mana wajen bunkasa sana'o'i daban-daban da kyautata tsarin tattalin arzikinmu. Shigowar kamfanonin kasar Sin za ta kawo karfin takara sosai ga kamfanonin wajenmu, abin da zai kawo amfani sosai ga bunkasuwar karfin takarar kamfanoninmu."(Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China