in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta lashi takobin kare 'yancin bin addini
2018-04-03 11:08:40 cri

Kasar sin ta lashi takobin ci gaba da kare 'yanci tare da mutunta al'ummarta mabiya addinai.

Wata takardar rahoto da majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar a hukumace, wadda aka yi wa taken 'dabarun kasar Sin game da kare 'yancin bin addini' ta ce, matsayinta na kasa mai tsarin gurguzu karkashin shugabancin JKS,kasar Sin ta dauki dabaru kan 'yancin bin addini bisa yanayi na kasa da na addini domin kare hakkin 'yan kasar na yin addini da samar da kyakkyawar alaka tsakanin mabiya addinai daban-daban da tabbatar da zaman lafiya ta fuskar addini da zaman takewa.

Takardar ta ce, kare hakkin bin addini da kula da dangantakar da ta shafi addini da dacewarta da zamani da yaki da kaifin kishin addini, ayyuka ne na bai daya dake gaban dukkan kasasehen duniya.

Ta kara da cewa, kasar Sin za ta daukaka sharadin dake cewa dole ne addini ya dace da kasar, sannan za ta samar da hanyoyin da addinai za su bi, ta yadda za su dace da tsarin gurguzu.

Manyan addinai da ake bi a kasar Sin sun hada da na Buddah da Tao da Islama da Katolika da Protestant, inda adadin mabiya addinan ya kai miliyan 200 da kuma malaman addinai sama da 380,000. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China