in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila da MDD sun cimma yarjejeniya kan 'yan ci ranin Afrika
2018-04-03 10:31:20 cri

Ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce kasar ta cimma yarjejeniya da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, domin soke shirinta na tasa keyar 'yan ci ranin Afrika dake neman mafaka a kasar.

Wata sanarwa da ofishin ya fitar jiya, ta ce karkashin wata yarjejeniya ta shekaru 5, hukumar kula da 'yan gudun hijira za ta taimaka wajen sake tsugunar da a kalla 'yan ci rani 16,250 galibi 'yan kasashen Eritrea da Sudan zuwa kasashen yamma.

Sauran kuma za su samu halaccin zama a Isra'ila, kuma gwamnatin za ta samar musu da horo kan sana'o'in hannu, tare da taimaka musu wajen neman aiki.

Sabuwar yarjejeniyar ta soke shirin gwamnatin kasar na korar dubban 'yan ci rani daga kasashen Eritrea da Sudan zuwa Uganda da Rwanda ko kuma tsare wadanda suka ki komawa har sai baba ta gani.

Alkaluman da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta fitar ya nuna cewa, Isra'ila na da 'yan ci ranin Afrika 42,000 wadanda galibinsu ke zama a wasu yankuna marasa kyau dake makwabtaka da kudancin Tel Aviv.

Hukumomi a kasar na ganin su a matsayin barazana ga asalin kasar a matsayin ta Yahudawa, inda aka dauki tsauraran matakai a kan su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China