in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al-Shabaab ta hallaka wasu jami'ai biyu a Mogadishu
2018-04-02 10:03:13 cri
Kungiyar masu tsattsauran ra'ayi a Somali, Al-Shabaab, ta hallaka wasu jami'ai 2 a birnin Mogadishu mai fama da rikici da yammacin ranar Asabar a wani hari na baya bayan nan data kaddamar a kasar ta gabashin Afirka.

A wata sanarwa da mayakan suka fitar ta kafar yada labarai mai nasaba da kungiyar sun sanar cewa, sune suka hallaka Hassan Indha-Dhuh da Mohamud Moallim Hassan Fagase wadanda manyan jami'ai ne a gundumar mulki ta Hamarweyne dake yankin Banadir.

'Yan sandan Somali sun tabbatar da mutuwar jami'an biyu, sai dai sun ce ana cigaba da gudanar da bincike domin zakulo maharan wadanda suka tsere daga wajen bayan da suka kaddamar da harin.

A wani labarin kuma, dakarun wanzar da tsaro na kungiyar tarayyar Afrika sun dakile wani harin da kungiyar Al-Shabaab ta yi yunkurin kaddamarwa a wani sansanin soja da ke kudancin Somalia a ranar Lahadi.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China