in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya yi shawarwari da takwaransa na Namibiya
2018-03-30 11:03:44 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Namibiya wanda ke ziyara a kasar Sin, jiya Alhamis a nan birnin Beijing. Wannan shi ne karo na biyu da shugaba Xi ya gana da shugaban kasar Afirka a cikin mako guda da ya gabata, inda a ranar 22 ga wannan wata, ya gana da takwaransa na kasar Kamaru Paul Biya a nan Beijing.

Yayin ganawar tsakaninsa da shugaba Hage Geingob na Namibiya, Xi ya bayyana cewa, babbar moriyar kasar Sin da ta kasashen Afirka suna dogara ne da juna, a don haka ya kamata sassan biyu su yi kokari tare domin karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.

Yayin ganawa da shugaban Namibya Hage Geingob, shugaba Xi ya bayyana cewa, zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Namibiya yana kara zurfi sannu a hankali, haka kuma zumuncin dake tsakanin jam'iyyun mulki na kasashen biyu yana kara karfafuwa a kai a kai, kana kasashen biyu suna gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu yadda ya kamata. Ya ce kasar Sin na daukar Namibya a matsayin aminiya a ko da yaushe, shi ya sa take son su hada hannu domin ciyar da huldar dake tsakaninsu gaba kamar yadda ake fata, a cewarsa, "A halin da ake ciki yanzu, gwamnatin kasar Sin ta dukufa kan aikin gina kasa, ita ma a nata bangaren, kasar Namibya na kokarin gaggauta raya masana'antu tare kuma da zamamintar da kanta, ana iya cewa, tana juyin juya hali karo na biyu a kasar, domin cimma burin samun 'yancin kai a fannin ci gaban tattalin arziki da kuma kawar da talauci a fadin kasar. kasar Sin tana son hada hannu da Namibiya domin kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannoni da dama, ko shakka babu hakan zai amfanawa al'ummun kasashen biyu baki daya."

A nasa bangare, a madadin gwamnatin Namibya da jama'ar kasarsa, shugaba Geingob ya taya shugaba Xi murnar sake zabarsa da aka yi a matsayin shugaban kasar Sin, sannan ya na taya shugaba Xi murnar babban sakamakon da kasar Sin ta samu karkashin jagorancin jam'iyyar JKS da kuma gwamnatin kasar ta Sin, ya kara da cewa, kasarsa tana mai da hankali matuka kan huldar dake tsakaninta da kasar Sin, kuma ita ma tana fatan za a daga matsayin huldar dak tsakaninsu, yana mai cewa, "Namibiya tana mai da hankali matuka kan huldar dake tsakaninta da kasar Sin. Duk da cewa, an samu manyan sauye-sauye game da yanayin da kasashen duniya ke ciki, huldar tana da tafiya lami lafiya, yanzu haka muna fatan za a daga matsayin huldar zuwa wani sabon mataki, kana muna fatan za a kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu a fannonin gina kayayyakin more rayuwar jama'a da horas da kwararru da musayar al'adu da ba da ilmi da sauransu. Hadin gwiwar dake tsakanin sassan a wadannan fannonin zai sake shaida cewa, cudanyar dake tsakanin kasashen biyu tana da babbar ma'ana."

Shugabannin kasashen biyu wato Sin da Namibiya sun tsai da kudurin cewa, za su kafa huldar hadin gwiwa mai sada zumunta bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni a tsakaninsu, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata Sin da Namibiya su kara karfafa cudanya tsakanin manyan jami'ansu da amincewa juna a fannin siyasa da musayar ra'ayoyi kan harkokin duniya, tare kuma da kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, ta yadda za su kiyaye babbar moriyar kasashen Afirka da sauran kasashe masu tasowa baki daya. Xi ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta na maraba da Namibiya ta shiga aikin aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, domin samun ci gaba tare.

Bayan shawarwarin, an daddale wasu takardun hadin gwiwa dake tsakanin sassan a gaban shugabannin biyu.

Mai ba da taimako ga ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong ya shaidawa wa manema labarai cewa, shugabannin kasashen biyu sun yabawa rawar da tsarin dandalin tattaunawar dake tsakanin Sin da Afirka ke takawa yayin da ake kokarin ingiza hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu. Kana shugaba Xi ya gayyaci shugaba Geingob ya halarci taron kolin dandalin da za a gudanar a nan birnin Beijing a watan Satumba mai zuwa, inda shugaba Geingob shi ma ya bayyana cewa, yana sa ran sake zuwansa nan kasar Sin. Chen Xiaodong ya bayyana cewa, "Har kullum kasar Sin tana ba da muhimmanci kan huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka, shugaba Xi shi ma ya jaddada cewa, Sin da Afirka suna da kyakkyawar makoma iri daya, ko shakka babu Sin da kasashen Afirka 'yan uwa ne, kuma abokai ne, hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu zai samu babban ci gaba bayan kokarin da suke a sabon zamanin da ake ciki."

Bisa gayyatar da shugaba Xi ya yi masa, shugaba Geingob yana ziyarar aiki a nan kasar Sin tsakanin ranekun 28 ga wannan wata zuwa 3 ga wata mai zuwa, wannan shi ne ziyara karo na 6 da ya kawo kasar Sin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China