Kafar watsa labarai ta kasar Masar Al-Ahram ta bayyana a shafin ta na yanar gizo cewa, shugaba Al Sisi ya samu yawan kuri'u da suka kai miliyan 23. Kafar ta kara da cewa, abokin hamayyar shugaban mai ci Moussa Mostafa Moussa, wanda ba wani sanannen dan siyasa ba ne, ya samu kuri'un da ba su wuce kaso 3 bisa dari ba.(Saminu Alhassan)