in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kara dankon zumunci tsakanin Sin da Afirka don kyautata makomar hadin kansu
2018-03-29 14:51:22 cri

Karon farko ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da manufar "kulla dangantaka da kasashen Afrika bisa gaskiya da kauna da yarda da aminci" da kuma dabarar "cimma muradu da kuma martaba ka'idoji", bayan ya ziyarci kasashen Afirka a matsayinsa na shugaban kasar Sin a watan Maris na shekarar 2013, lamarin da ya nuna wata hanya ta bunkasa dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka a wannan sabon zamani da muke ciki. A cikin wadannan shekaru biyar da suka gabata, Sin da Afirka sun hada kansu cikin sahihanci sosai, duba da yadda suka kara dankon zumunci a tsakaninsu da mai da hankali kan samun ci gabansu gaba daya, da kuma kara fahimtar juna a siyasance. Haka kuma sakamakon ingantuwar dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu, yanzu nahiyar Afirka ta na samun ci gaba a fannoni daban daban.

A ranar 25 ga watan Maris din shekarar 2013 ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani jawabi mai taken "zama aminai cikin sahihanci har abada" a kasar Tanzania, inda ya bayyana manufofin kasar Sin na neman samun zaman lafiya da ci gaba tare da kasashen Afirka. Shugaba Xi ya ce, za mu nuna gaskiya ga aminanmu na Afirka, za mu kuma dauki matakai na a zo a gani wajen hadin kanmu, game da zumunci kuwa za mu kara nuna kauna ga juna, yayin da muke warware matsalolin da ke cikin ayyukan hadin kanmu, za mu nuna sahihanci ga juna.

Daga baya kuma a watan Disamban shekarar 2015, an kira taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka a Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, lamarin da ya kara ciyar da huldar da ke tsakanin bangarorin biyu gaba. Sabo da a yayin taron kolin, kasar Sin ta gabatar da manyan ginshikai biyar da kuma shirye-shirye goma na hadin gwiwar Sin da Afirka. Bangarorin biyu kuwa sun amince da cewa, za su daukaka dangantakarsu zuwa ta abota da hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, hakan zai bukaci su zama daidai wa daida da amincewa juna ta fuskar siyasa, da hadin kansu don moriyar juna ta fuskar tattalin arziki, da kara cudanya da juna a fannin al'adu, da taimakawa juna a fannin tsaro, gami da hadin gwiwarsu cikin harkokin duniya.

Sin, kasa ce mafi girma da ke tasowa a duniya, Afirka kuma nahiya ce da aka fi samun yawan kasashe maso tasowa. Hakan ya sa Sin da Afirka ke rike da hannun juna sosai. Daga manufar "kulla dangantaka da kasashen Afrika bisa gaskiya da kauna da yarda da aminci" zuwa manyan ginshikai biyar na hadin kansu, yanzu dankon zumuncin da ke tsakanin Sin da Afirka na kara kyautatuwa, wanda zai samar wa Afirka wata makoma mai haske.

A lokacin da cutar Ebola ta barke a yammacin kasashen Afirka a shekarar 2014, kasar Sin ta dauki matakai ba tare da bata lokaci ba, inda ta tura kwararru a fannin yaki da cuttuka masu yaduwa da ma'aikata masu aikin jinya zuwa kasashen Guinea da Laberiya da Saliyo, don yaki da annobar cutar. A shekarar 2016, Sauyin yanayi na El Nino ya haddasa mutuwar 'yan kasar Habasha fiye da miliyan goma sakamakon yunwa, don haka, kasar Sin ta samar da gundummawar abinci cikin lokaci.

Lamuran kuwa abin shaida ce na dangantakar kud-ta-kud a tsakanin Sin da Afirka, kuma muhimmin dalili ne na kara kyautatuwar matsayin hadin kansu.

Taimakon da kasar Sin ta bayar cikin halin gaggawa, da ayyukan more rayuwar jama'ar Afirka bisa hadin gwiwar Sin da Afirka, kamar su hanyoyin mota, layoyin dogo dukkansu sun sheda dankon zumunci da ci gaban bangarorin biyu. A sabo da wadannan ayyukan, tattalin arziki na wasu kasashen Afirka ya samu saurin bunkasuwa.

A cikin wadannan shekaru da suka gabata, an riga an kammala yawancin ayyukan da ke cikin shirye-shirye goma na hadin kan Sin da Afirka kafin lokacin da aka tsara, wadanda suka amfana wa jama'ar Afirka sosai.

Layin dogo a tsakanin Mombasa da Nairobi na kasar Kenya da aka kaddamar da amfani da shi a ranar 31 ga watan Mayu na shekarar 2017 wani muhimmin sakamako ne da aka samu wajen aiwatar da shirye-shiryen goma. Yayin da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi rangadin aiki ga layin dogon, ya bayyana cewa, layin dogon zai taimakawa Kenya a yunkurinta na raya masana'antu, ta yadda kasarsa za ta samu sauyin salon tattalin arziki.

A watan Satumban bana, za a kira taron koli na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka a nan birnin Beijing, inda za a dora muhimmanci kan hadin gwiwar bangarorin biyu bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" domin raya makomarsu bai daya. Sa'an nan za a hada shawarar da ajandar neman samun dauwamammen ci gaba na MDD nan da shekarar 2030, da ajandar kungiyar AU na nan da shekarar 2063, da tsare-tsaren ci gaban kasashen Afirka baki daya.

Yayin da ake kokarin samun ci gaba bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", kasashen Afirka na taka muhimmiyar rawa. Sin da Afirka na iya ba da babban taimako ga juna ta fuskar tattalin arziki. Bisa wannan shawarar, za su iya hada manyan tsare-tsarensu na neman samun bunkasuwa tare, hakan zai samar wa Afirka albarkatu da hanyoyi da kasuwa wajen zamanintar da nahiyar.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China