in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen duniya sun mai da hankali kan ziyarar shugaban DPRK a Sin
2018-03-29 13:58:15 cri

Kasashen duniya sun dora muhimmanci kan ziyarar da shugaban jamhuriyar Koriya ta Arewa (DPRK) Kim Jong Un ya kai kasar Sin, wace ziyara ce ba a hukumance ba, wadda ake daukar ta a matsayin babban ci gaba ne wajen sassauta yanayin da ake ciki game da batun zirin Koriya.

Domin amsa goron gayyatar Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, mista Kim, shugaban jam'iyyar Workers' Party ta Koriya ta Arewa, kuma shugaban kasar DPRK, ya kai ziyarar kasar Sin daga ranar Lahadi zuwa Laraba.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, tana maraba da ganawar shugabannin na Sin da DPRK, kana ta jaddada goyon bayan ci gaba da aiki cikin hadin gwiwa da kasar Sin domin samun nasarar warware rikicin yankin arewa maso gabashin nahiyar Asiya ta hanyar siyasa, da matakan diplomasiyya, ta hanyar tattaunawar kai tsaye tsakanin dukkanin bangarorin da abin ya shafa.

Ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Kudu ma ta yaba wa tattaunawar da aka gudanar tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da na Koriya ta Arewa Kim Jong Un, kuma ana sa ran ziyarar ta mista Kim a kasar Sin za ta taimaka wajen warware matsalar hana kera makaman nukiliyar da kuma wanzar da zaman lafiya mai dorewa a zirin Koriyar.

Kamfanin dillancin labaran Koriya ta Arewa (KCNA), da kamfanin dillancin labarai mallakar kasar Rasha Rossiya Segodnya, da Yonhap na Koriya ta Kudu, da Kyodo na Japan da sauran manyan kamfanonin dillancin labarai na duniya sun ba da rahotanni game da ziyarar Kim zuwa kasar Sin da kuma tattaunawarsa da shugaba Xi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China