in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sudan ya tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta a yankunan dake fama da rikici da watanni 3
2018-03-29 10:42:12 cri
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir, ya gabatar da umarnin tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta a yankunan dake fama da rikici da watanni 3.

Kamfanin dillancin labarai na kasar SUNA ya ruwaito cewa, shugaba Al-Bashir ya sanar da matakin ne a jiya, inda ya tsawaita wa'adin har zuwa ranar 30 ga watan Yunin bana.

Cikin 'yan shekarun da suka gabata, gwamnatin Sudan da bangaren adawa, sun ci gaba da sabunta wa'adin tsagaita bude wuta a yankunan kasar dake fama da rikici.

Shugaba al-Bashir ya fara ayyana tsagaita bude wutar ne a watan Yunin 2016 na tsawon watanni 4, da nufin ba 'yan tawayen damar zirga zirga don halartar taron tattaunawa ta kasa, daga bisani kuma aka kara tsawaita wa'adin sau da dama.

Tun a shekarar 2011 Gwamnatin Sudan ke yaki da 'yan tawayen SPLM na bangaren arewacin kasar a yankunan Blue Nile da Kordofan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China