in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dubban 'yan Ghana sun yi zanga zangar adawa da yarjejeniyar hadin gwiwar tsaron Ghana da Amurka
2018-03-29 09:50:39 cri

A jiya Laraba dubun dubatar 'yan kasar Ghana karkashin inuwar kungiyar fafutuka ta 'Put Ghana First Movement' sun yin gangami a manyan titunan kasar domin yin zanga zangar nuna adawa da yarjejeniyar hadin gwiwar wanzar da tsaro tsakanin kasar Ghana da Amurka wato (DCA), wanda majalisar dokokin kasar ta amince da ita.

Bernard Mornah, shugaban kungiyar PNC ta kasar Ghanan, ya fayyace wa dandazon masu zanga zangar cewa, matakin zai jefa kasar Ghanan cikin tsaka mai wuya.

Ya jaddada cewa kasancewar al'ummar kasar ta Ghana suna rayuwa ne karkashin dokokin kasarsu, don haka duk wani 'dan kasar wajen dake son rayuwa ko aiki a cikin kasar ta Ghana, ciki har da sojojin Amurka, dole ne su kiyaye dokokin cikin gidan kasar.

Kungiyar daliban kasar Ghana (NUGS), wanda ta kunshi dukkan daliban jami'o'in kasar, suna daga cikin wadanda suka halarci zanga zangar ta ranar Laraba.

Shugaban kungiyar NUGS, Elisha Oheneba Essumang, ya yi gargadin cewa, za su ci gaba da zanga zangar, har zuwa lokacin da za'a soke yarjejeniyar.

Tsohon jakadan kasar Ghana a Amurka, Ekwow Spio-Garbrah, ya lura cewa, yarjejeniyar tana shan suka a cikin gida da kasashen ketare, inda ake bayyana ta da cewa, ta saba da muradun al'ummar kasar ta Ghana.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China