in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Iraqi ya ce kasar sa na nisanta kan ta daga takaddamar dake tsakanin Amurka da Iran
2018-03-28 20:01:56 cri

Firaministan Iraqi Haider al-Abadi, ya ce kasar sa na fatan nisanta kan ta daga takaddamar dake tsakanin Amurka da Iran. Al-Abadi wanda ya yi wannan tsokaci a Larabar nan, yayin taron bunkasa makamashi na Iraqin da ya gudana a birnin Bagadaza, ya ce kasar sa ba ta son goyon bayan wani bangare, tana kuma fatan kyautata dangantakar ta da kasashen Amurka da Iran.

Ya ce wannan matsaya ita ce za ta amfani kasar sa, yana kuma fatan Amurka ba za ta janye daga yarjejeniyar makaman nukiliyar Iran ba, duba da cewa yarjejeniyar na share fagen kawo karshen takaddamar da ake yi, game da shirin kasar na mallakar makaman kare dangi.

Kalaman Abadi dai na zuwa ne, yayin da ake ci gaba da fuskantar halin rashin tabbas game da wannan yarjejeniya ta nukiliyar Iran, inda tuni shugaban Amurka Donald Trump ya fara nuna ra'ayin sa, na yiwuwar ficewa daga waccan yarjejeniya da aka kulla tun a shekarar 2015, muddin dai ba a yi sauye sauye wadanda za su kyautatawa Amurkan ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China