in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Afirka suna hada kansu domin samun nasara tare
2018-03-28 13:45:49 cri

Kwanan baya, Zhou Yuxiao, jakadan kasar Sin mai kula da harkokin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka FOCAC ya bayyana a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya cewa, kasar Sin da kasashen Afirka suna hada kansu domin samun nasara tare, a maimakon kira take kawai.

Kafin a sallami Rex Tillerson daga mukaminsa na sakataren harkokin wajen kasar Amurka, ya taba ziyartar kasashen Habasha, Djibouti, Kenya, Chadi da Nijeriya a watan Maris na bana. Kafin tafiyarsa zuwa Afirka da kuma lokacin ziyararsa, ya zargi kasar Sin cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ta sanya Afirka ta dogaro da sauran kasashe, ta kuma raunana ikon mulki kan kasashen na Afirka, tare da kara basussukan da ake binsu. Dangane da kalamansa, Zhou Yuxiao, jakadan kasar Sin mai kula da harkokin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka ya musunta kalaman nasa.

Yayin da yake zantawa da manema labaru, Zhou Yuxiao ya yi nuni da cewa, kasar Sin da kasashen Afirka suna hada kansu domin samun nasara tare, a maimakon kira da take kawai. "Kasashen Sin da Afirka suna hada kansu ne ba tare da son zuciya ba. Suna kokarin samun nasara da ci gaba tare. Hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ta zama abin misali a fannin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama. Abun da kasar Sin ke yi shi ne taimakawa kasashen Afirka wajen kyautata karfinsu na samun ci gaba mai dorewa. Kasar Sin na zuba jari a nahiyar Afirka da kara yawan ababen more rayuwar jama'a, da kuma masana'antu, lamarin da yake taimakawa kasashen Afirka kara karfin kera kayayyaki da rage basussukan da ake binsu."

Dangane da basussukan da ake bin kasashen Afirka yayin da suke kokarin bunkasa kansu, Zhou Yuxiao ya ce, "Bunkasar masana'antu, hanya ce mafi dacewa wajen biyan basussukan da ake bin kasashen Afirka. In babu kudi, yaya za a raya kasa? A baya, kasar Sin ta jawo yawan jarin waje ne sakamakon bude kofa ga kasashen waje tare da yin gyare-gyare a gida. Mun zabi kasar Kenya kamar misali, Kenya ta samu rancen kudi daga kasar Sin ta shimfida layin dogo daga Mombasa zuwa Nairobi. Yanzu ta fara amfani da ita, nan gaba za a kafa yankunan tattalin arziki a wuraren da aka shimfida layin dogon, tare da bunkasa aikin sufurin kayayyaki. Bunkasar tattalin arziki ta taimakawa Kenya wajen biyan bashi."

A tsakiyar watan Maris na bana, Zhou Yuxiao da wasu kwararru da masana daga hukumomin nazarin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka sun ziyarci kasashen Habasha, Uganda da Kenya, inda suka yi musayar ra'ayoyi da jami'ai da masana na kasashen 3 dangane da yadda za a gudanar da taron kolin Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, sa'an nan sun yi taron bita tare da 'yan kasuwan kasar Sin dake Afirka. Zhou ya nuna cewa, ana nuna himma da kwazo kan hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka. Sun kuma amince da sakamakon kyakkyawar hadin gwiwar.

A ranar 8 ga watan Maris, yayin da Rex Tillerson, tsohon sakataren harkokin wajen kasar Amurka a wancan lokaci ya ziyarci babban zauren kungiyar tarayyar Afirka da ke birnin Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha, inda ya ce, ya yi fatan cewa, kasashen Afirka za su yi tunani sosai kan alakar dake tsakanin ikon mulkin kasa da kuma yarjejeniyoyin da suka daddale da kasar Sin. Dangane da bayaninsa, Zhou Yuxiao ya ce, "A ganina, taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, ya yi kama da littafin jagora ne wajen daukar matakai da samun ci gaba. Za a dauki matakan a-zo-a-gani ne a maimakon kira da take da yin ihu kawai. Idan wasu sun yi kalamai kamar haka kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, sai na ba su shawarar yiwa kasashen Afirka wani abu. Idan kasashen Afirka da jama'ar Afirka ba su son hanyar da ake bi wajen yin hadin gwiwa da Sin da kuma sakamako da aka samu, to, za su bayyana mana ra'ayoyinsu da bakinsu." (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China