in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na son ci gaba da wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo
2018-03-28 11:03:29 cri
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya, Wu Haitao, ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da kasashen duniya domin ci gaba da taka rawar a-zo-a-gani wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo.

Kwamitin tsaron MDD ya zartas da wani kuduri a jiya Talata, inda aka tsawaita wa'adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya da MDD ta jibge a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo.

Mista Wu ya ce, wannan tawaga ta taka muhimmiyar rawa a fannin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kongon. Ya kamata kasashen duniya su ci gaba da mara mata baya, don haka kasar Sin ta jefa kuri'ar amincewa da kudurin tsawaita wa'adin aikin tawagar a Kongon.

Wu ya kara da cewa, a ganin kasar Sin, yayin da kasashen duniya ke baiwa Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo tallafi da taimako, ya zama dole a mutunta ra'ayin gwamnatin kasar, da girmama ikon mallakar kasar gami da cikakken yankinta, da taimakawa kasar wajen inganta karfinta domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali bisa karfin kanta.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China