in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta bukaci a zauna a teburin sulhu domin warware takaddama kan batun tekun Habasha
2018-03-28 10:06:16 cri
A jiya Talata kasar Sudan ta jaddada muhimmancin cigaba da hawa teburin tattaunawar sulhu tsakanin kasashen Sudan, Masar da Habasha, domin warware sabani da kuma cimma gamsasshiyar matsaya game da takaddamar da ta kaure tsakanin bangarorin game da batun tekun Habasha wato (GERD).

A jiya Talata ne ministan harkokinn wajen Sudan Ibrahim Ghandour, ya karbi bakuncin wata tawaga daga kasar Amurka karkashin jagorancin Eric Stromayer, mataimakin sakataren cibiyar kula da al'amurran Afrika ta kasar Amurka, wanda a halin yanzu yake ziyarar aiki a kasar ta Sudan da nufin lalibo bakin zaren warware takaddama kan batun tekun na GERD.

A cewar wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Sudan din ta fitar, Ghandour, ya nanata muhimmancin ci gaba da tattaunawar sulhu da kuma yin aiki tukuru domin cimma matsaya da samun sakamako mai gamsurwa tsakanin dukkan bangarorin da abin ya shafa.

Haka zalika ya sake jaddada muhimmancin gudanar da taron ministocin harkokin wajen kasashen uku, da ministocin neman rani na kasashen, da kuma manyan jami'an hukumomin tattara bayanan sirri, da jami'an tsaro na kasashen uku, wanda aka shirya gudanarwa a Khartoum a watan Afrilu. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China