Hukumomin tsakiya na kasar sun fitar da wasu tsare-tsare da za su bunkasa kudin shiga da matsayin ma'aikata masu basira.
Za kuma a karfafa gwiwar gudanar da sana'o'i don kara jan hankalin ma'aikata, ciki har da ba su karfin fada a ji a harkokin gudanar da ma'aikatu da albashi mai tsoka da damar sayen hannayen jari. Gwamnati za ta kuma ba ma'aikatan lakabi na alfarma tare da ba su kulawa ta musamman a fannonin samun gidaje da ilimin yaransu.
Kasar Sin na fatan dabarun za su ba ma'aikata kwarin gwiwar inganta basirarsu da kirkiro abubuwa ta yadda za su ja hankalin matasa masu basira zuwa ga ayyukan hannun wadanda suka shafi harhada abubuwa da gyare-gyare da gine-gine da sauransu.
A cewar mataimakin ministan kula da harkoki da tsaron al'umma na kasar Tang Tao, wannan ne karon farko da kasar Sin ta bada gagarumin muhimmanci kan wannan batu. (Fa'iza Mustapha)