in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya ce ya dace Sin da Amurka su sa kaimi kan daidaiton cinikayya
2018-03-27 10:35:30 cri


Jiya Litinin a nan birnin Beijing firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya yi ganawa da wakilan kasashen waje wadanda suka halarci taron shekara ta 2018 na dandalin raya kasar Sin, inda suka yi tattaunawa kan batun cinikayyar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka.

Yayin ganawar, firaiministan kasar Sin Li Keqaing, ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, an lura cewa, cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka tana habaka cikin sauri, dalilin da yasa haka shine domin bukatun kasuwannin kasa da kasa, haka kuma domin ka'idojin kasuwancin da ake bi, ana iya cewa, sassan biyu sun samu babbar moriya daga wajen, idan cinikayyar dake tsakanin sassan biyu ta gamu da matsala, ko shakka babu ba wanda zai samu moriya daga wajen. Yanzu haka Sin da Amurka suna fama da rashin daidaiton cinikayya, kamata ya yi sassan biyu su yi hakuri su yi hangen nesa kuma su yi kokarin sa kaimi kan daidaiton cinikayya ta hanyar kara habaka cinikayyar dake tsakaninsu, to, idan sassan biyu suna son warware rigingimu a fannin, ya fi dacewa su gudanar da shawarwari.

Yayin tattaunawar, wakilan da suka zo daga kamfanin Apple na Amurka da kamfanin Hitachi na Japan da rukunin zuba jari na Starr na Amurka da kamfanin Google na Amurka da jami'ar Cambridge ta Birtaniya da kamfanin Gualcomm na Amurka da sauran manyan kamfanonin kasa da kasa sun gabatar da tambayoyi ga firayin minista Li Keqiang, daya bayan daya kuma Li ya basu amsa.

Maurice Greenberg, shugaban rukunin zuba jari na Starr na kasar Amurka ya tambayi firayin minista Li game da rigingimun cinikayyar wanda Sin da Amurka suke gamuwa dashi a halin yanzu, Li Keqiang ya nuna cewa, cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka tana habaka cikin sauri, dalilin da ya sa haka shine domin bukatun kasuwannin kasa da kasa, haka kuma domin ka'idojin kasuwancin da ake bi, ana iya cewa, sassan biyu sun samu babbar moriya daga wajen, idan cinikayyar dake tsakanin sassan biyu ta gamu da matsala, ko shakka babu ba wanda zai samu moriya daga wajen, a cewarsa, "Kamata ya yi kasashen duniya su yi kokari tare domin kiyaye tsarin cinikayya dake tsakanin bangarori da dama, haka kuma su yi adawa ga ra'ayin bada kariya ga cinikayyar wata kasa ita kadai, ba wanda zai samu moriya daga wajen rigingimun cinikayya, yanzu ya kasance rashin daidaiton cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka, a don haka ya dace sassan biyu su yi hakuri su yi hangen nesa, kuma su yi kokarin sa kaimi kan daidaita cinikayya ta hanyar kara habaka cinikayyar dake tsakaninsu, kuma su daidaita matsalar ta hanyar yin shawarwari, in ba haka ba, lamarin zai lahanta moriyar kasashen biyu, har zai lahanta moriyar daukacin kasashen duniya baki daya."

Li ya ci gaba da cewa, bude kofa ga kasashen waje babbar manufa ce da kasar Sin ke aiwatarwa, nan gaba kasar Sin zata kara zurfafa kwaskwarima a fadin kasar a karkashin jagorancin babban sakataren JKS Xi Jinping, yana mai cewa, "Bana shekaru 40 kenan cif cif da aka fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin, nan gaba kasar Sin zata kara bude kofa ga kasashen waje, saboda hakan ya dace da moriyar kasar Sin, kuma hakan zai taimaka kan aikin tabbatar da cinikayya maras shinge, tare kuma da ciyar da bunkasuwar kasashen duniya gaba yadda ya kamata, muna son koyon fasahohin zamani na kasashen waje yayin da muke habaka hadin gwiwar dake tsakaninmu da sauran kasashen duniya, musamman ma a fannonin samar da kayayyaki da bada ilmi da samar da fasahohin zamani da hidima."

Yanzu ana kokari domin cimma burin kasancewa babbar kasa wajen kera na'urori nan da shekarar 2025, Li ya bayyana cewa, yana maraba da fitattun kamfanonin kasashen waje su zo nan kasar Sin domin gudanar da hadin gwiwa, ta yadda zasu samu ci gaba tare da kamfanonin kasar Sin, Li ya ce, "Ana gudanar da shirin kasancewa babbar kasa wajen kera na'urori nan da shekarar 2025 ne a cikin muhallin bude kofa, muna amfani da ma'auni iri daya yayin da muke gudanar da hadin gwiwa da kamfanonin Sin da waje, haka kuma zamu kara kiyaye ikon mallakar fasaha."

Wakilai mahalartan taron sun bayyana cewa, suna cike da imani ko shakka babu ci gaban kasar Sin zai kawo damammaki ga ci gaban kasashen duniya, mai jagorancin kamfanin Apple Tim Cook ya ce, "Mun godewa firayin minista Li Keqiang matuka saboda ya yi tattaunawa a fili tare da mu, bana shekaru 40 kenan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima da bude kofa, muna fatan kasar ta Sin za ta kara bude kofa a nan gaba."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China