in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
In dai har an lalata moriyar kasar Sin, ko shakka babu za ta dauki matakai, in ji ma'aikatar kasuwanci
2018-03-26 13:35:57 cri

A ranar 22 ga wata ne, shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sa hannu a kan takardar bayani, inda bisa ga binciken rahoto mai lamba 301 da ofishin kula da harkokin cinikayya na kasar Amurka ya bayar, ya umarci sassan da abin ya shafa da su dauki matakai na kayyade harkokin ciniki a tsakanin kasar ta Amurka da kasar Sin. A game da wannan, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin a ranar 23 ga wata ta bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta dauki matakai, in dai har an lalata moriyarta.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump a ranar 22 ga wata ya sa hannu kan takardar bayani, inda bisa ga sakamakon bincike mai lamba 301, za a sanya haraji a kan dimbin kayayyakin da take shigowa daga kasar Sin, tare kuma da kayyade harkokin zuba jari da kamfanonin kasar Sin ke yi a Amurka. Shugaba Trump kafin ya sa hannu, a fadar White House ya bayyanawa kafofin yada labarai cewa, yawan kayayyakin kasar Sin da haraji ya shafa zai iya kai dalar Amurka biliyan 60.

Shugaban sashen kula da yarjejeniyoyi da dokoki na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, Chen Fuli a ranar 23 ga wata ya bayyana cewa, "Binciken da Amurka ta gudanar ya yi fatali da ainihin yanayin cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka. Huldar ciniki ta bunkasa da sauri a yayin da Sin ke aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje. A shekarar 2017 kadai, yawan cinikin kayayyakin dake tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka biliyan 580, a yayin da yawan cinikin hidimomi ya kai dalar Amurka biliyan 120. Sa'an nan, yawan jarin da sassan biyu suka zubawa juna gaba daya ya zarce dalar Amurka biliyan 230. Alakar kasashen biyu ta fannin cinikayya na kara karfafuwa. Sai dai binciken mai lamba 301 da Amurka ta gudanar ta bada misali maras kyau, matakin da ba zai amfanawa moriyar kasar Sin ba, haka kuma ba zai amfanawa Amurkar ko kasashen duniya ba."

A ranar 23 ga wata, kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya ce, Amurka ta yi biris da matakan da kasar Sin ta dauka na inganta aikin kare hakkin mallakar ilmi, haka kuma ta yi fatali da dokokin kungiyar cinikayya ta duniya da kiran da masu ruwa da tsaki suka yi, inda ta kare aniyarta, matakin da a zahiri dai na kariyar ciniki ne, don haka, kasar Sin ta tashi tsaye wajen bayyana rashin amincewarta. Ko ta yaya, ba za ta bari a lalata moriyarta ba. A game da wannan, Chen Fuli ya ce, "Matsayin kasar Sin tsayayye ne wajen kare moriyarta ta halal. Sau da dama mu kan bayyana matsayinmu a kan binciken da Amurka ta gudanar, wato ba mu son yakin cinikayya, kuma ba za mu haddasa wani ba, amma ba mu jin tsoro in dai har wata ta tada rikicin, balle ma mu ja da baya. A hakika, a shirye muke mu dauki matakai na kare moriyarmu ta halal."

Har wa yau, a wata tattaunawar da jakadan kasar Sin da ke Amurka, Cui Tiankai ya yi tare da gidan talabijin na Bloomberg na kasar Amurka a ranar 23 ga wata, ya ce, a game da sakamakon binciken mai lamba 301 da Amurka ta samar da kuma matakan da ta dauka, kasar Sin na tunanin duk matakan da za ta iya dauka don kiyaye moriyarta ta halal.

Mr. Cui ya kara da cewa, kasashen Sin da Amurka na da kyakkyawar dama da kuma makoma ta yin hadin gwiwa, sai dai ya kamata su daidaita matsaloli da sabanin da suke fuskanta ta hanyar yin hadin gwiwa da shawarwari da juna, a maimakon nuna kiyayya. A hakika, kasashen biyu na yin shawarwari, don haka, yadda Amurka ita kanta ta dauki matakai a wannan lokaci ya sa mana rudani. Yadda kasar Sin ke samun rarar kudin ciniki da Amurka ba zai amfanawa Sin din ba, kuma kasashen biyu na da ra'ayi daya a kan batun tabbatar da daidaiton ciniki. Sin na son kara shigar da kayayyaki daga Amurka, amma ko Amurka din ta shirya?

A game da yadda Amurka ke zargin kasar Sin da satar hakkinta na mallakar fasaha da tilasta kamfanoninta su ba da fasahohinsu, jakadan ya ce, "Babu wata dokar kasar Sin da ta tilastawa kamfanonin ketare su bada fasahohinsu, kuma ana gudanar da ciniki ne bisa amincewa. Idan akwai kamfanonin da suke ganin an lalata hakkinsu na mallakar fasaha, lalle ya kamata mu gabatar da shaidu tare da kai kara, kuma Sin na son bada nata taimakon. Dokokin kasar Sin na kare hakkin mallakar ilmi, kuma bai dace ba a zargi wani ba tare da gabatar da shaida ba." (Lubabatu Lei)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China