in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan tawayen Houthi na Yemen sun harba makamai masu linzami zuwa filayen jiragen sama 4 na Saudiyya
2018-03-26 10:25:02 cri

Yan tawayen Houthi na kasar Yemen sun harba makamai masu linzami dake cin dogon zango, zuwa filayen jiragen sama na kasa da kasa guda 4 dake Saudiyya da tsakar daren jiya Lahadi.

Kamfanin dallancin labarai na SABA dake karkashin 'yan tawayen, ya ruwaito cewa, harin umarni ne daga shugaban kungiyar Abdul-Malik al Houthi, haka zalika, ramuwa ce kan dakarun kawance da Saudiyya ke jagoranta, na amfani da duk wani makami a yakin da suke a Yemen.

Kungiyar ta kara da cewa, ta kuma harba wasu makamai masu linzami zuwa wasu wurare a Saudiyyan, sai dai ba ta bayyana sunayen wuraren ba.

Hare-haren na zuwa ne jim kadan bayan shugaban 'yan tawayen Abdul-Malik al-Houthi ya gabatar da jawabi a talabijin, ta wasu tasoshi da kungiyar ke iko da su, domin tunawa da ranar da ake cika shekaru 3 da yakin da kungiyarsa ke yi da gwamnatin Yemen, dake samun goyon bayan kasashen duniya da kuma dakarun kawance da Saudiyya ke jagoranta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China