in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin MDD na kokarin shirya zagayen karshe na yarjejeniyar gyara tsarin siyasar Libya
2018-03-26 09:28:17 cri

Manzon musammam na MDD a Libya Ghassan Salame, ya ce zai yi yunkuri na karshe na shirya tattaunawa tsakanin bangarorin adawa na kasar Libya da nufin gyara yarjejeniyar siyasar kasar da MDD ke daukar nauyi.

Ghassan Salame, ya ce ya jaddadawa shugaban majalisar wakilan yankin gabashin kasar Agila Saleh, bukatar gaggauta gudanar da zabe kafin karshen shekarar nan.

Wakilin na MDD ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da Agila Saleh a birnin Al-Qubbah dake gabashin kasar, inda suka tattauna game da yanayin da siyasar kasar ke ciki a baya-bayan nan da kuma shirye-shiryen zaben dake karatowa.

Libya dai na fama da rarrabuwar kawuna sanadiyyar siyasa tsakanin gwamnatin gabashin kasar dake Tobruk da kuma ta gwamnatin yammacin kasar da MDD ke marawa baya, wadda mazauni a Tripoli. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China