in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyi a arewacin Nijeriya sun kada kuri'ar yanke kauna da shugabannin siyasa
2018-03-26 09:11:22 cri

Makomar 'yan siyasar arewacin Nijeriya dake son tsayawa takara a babban zaben kasar na shekarar 2019 na cikin halin kila-wa-kala, la'akari da muhimman kungiyoyi 17 na yankin da suka kada kuri'ar yanke kauna da shugaban kasar Muhammadu Buhari da sauran 'yan siyasar yankin.

Kungiyoyin karkashin jagorancin kungiyar tuntuba ta dattawan arewa da kungiyar dattawan arewa, sun ce shugaban kasar da sauran 'yan siyasar yankin sun gaza, duba da yadda suka kasa magance matsalolin da yankin ke fuskanta, ciki har da tsaro da fatara.

Wannan dai shi ne matakin da taron kungiyoyin arewar da ya gudana a ranar Asabar da ta gabata a birnin Kaduna ya cimma.

Kungiyoyin sun kuma yi gargadin cewa, kada wani dan siyasa ya sa ran za a zabe shi a babban zaben kasar mai zuwa, muddun ba nuna kudurinsa na cin nasara wajen yaki da fatara da rashin ci gaba a yankin ya yi ba

Nijeriya dai ta shirya gudanar da babban zabenta ne a watan Fabrerun shekarar 2019.

Tun a shekarar 2009 kasar ta fara fuskantar matsalar rashin tsaro, inda ta yi asarar rayuka sama da 20,000 a yankin na arewa, sanadiyyar ayyukan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China